Jami'an DSS Sun Mamaye Ofishin SERAP Awanni bayan Kungiyar Ta Nemi a Binciki NNPCL

Jami'an DSS Sun Mamaye Ofishin SERAP Awanni bayan Kungiyar Ta Nemi a Binciki NNPCL

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun mamaye ofishin kungiyar SERAP na babban birnin tarayya Abuja
  • SERAP ta bayyana cewa jami'an hukumar DSS sun bukaci ganawa da daraktocin kungiyar bayan mamaye ofishin nasu ba bisa ka'ida ba
  • Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta umarnin DSS ta fice daga ofishin nata bayan abin da ta kira da keta doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun karbe ikon ofishin kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke babban birnin tarayya Abuja.

Mamaye ofishin SERAP da jami'an DSS suka yi na zuwa ne awanni bayan da kungiyar ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye karin kudin fetur da kuma bincikar NNPCL.

Kara karanta wannan

'Ya isa haka': Ƴan kwadago sun dauki ɗumi bayan kama shugabansu

Jami'an DSS sun mamaye ofishin kungiyar SERAP na Abuja
SERAP ta nemi daukin Tinubu bayan jami'an DSS sun mamaye ofishinta na Abuja
Asali: Twitter

DSS sun mamaye ofishin SERAP

Kungiyar SERAP ce ta sanar da wannan samamen da jami'an DSS suka kai ofishinta a shafinta na X a ranar Litinin.

Kungiyar ta bayyana cewa kwace ikon ofishinta da DSS ta yi ya sabawa dokar kasa.

SERAP ta ce jami’an hukumar DSS bayan mamaye ofishinta, sun bukaci ganawa da daraktocin kungiyar.

Kungiyar ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki a wannan lamari.

SERAP ta nemi daukin Tinubu

Sanarwar da SERAP ta fitar ta ce:

"A halin yanzu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) sun mamaye ofishin SERAP da ke Abuja ba bisa ka’ida ba, suna neman ganin daraktocin mu.
"Ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya umarci hukumar SSS da ta gaggauta kawo karshen wannan cin zarafin, da kuma farmaki ga 'yancin 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kai samame cikin gari, sun buɗewa mutane wuta

"A janye karin kudin fetur" - SERAP

Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar da ke kare hakkin al'umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta ba Shugaba Bola Tinubu wa'adin awa 48 ya janye karin kudin fetur.

SERAP ta kuma bukaci shugaban kasar da ya kaddamar da binciken cin hanci da rashawa a kamfanin NNPCL wanda ta ce shi ne ke jawo cikas ga bangaren man kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.