Sojojin Najeriya Sun Kai Samame cikin Gari, Sun Buɗe Wa Mutane Wuta

Sojojin Najeriya Sun Kai Samame cikin Gari, Sun Buɗe Wa Mutane Wuta

  • Sojoji sun sake shiga garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar Delta da safiyar ranar Litinin 9 ga watan Satumba, 2024
  • Rahotanni sun ce sojojin sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, wanda ya tilastawa mazauna garin faɗawa dazuka domin tsira da rayuwarsu
  • Wani mazuanin garin ya ce tun ranar Lahadi sojojin suka turo jirage marasa matuƙa domin tattara wasu bayanai gabanin su shigo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Najeriya sun sake kai samame garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Wasu majiyoyi daga yankin sun yi iƙirarin cewa sojojin sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi da suka afkawa garin da safiyar yau Litinin, 9 ga watan Satumba, 2204.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wani asibiti a Kaduna, sun tafka ɓarna

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun kutsa cikin garin Okuama, sun kori mutane a jihar Delta Hoto: @DefenceinfoNG
Asali: Twitter

Rikicin Okuama: Sojoji sun kama shugabanni

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan na zuwa ne makonni ƙalilan bayan cafke wasu daga cikin shugabannin al'umma a garin.

Wani mazaunin garin ya ce dakarun sojojin sun biyo ta kauyen Okoloba suka afka Okuama bayan sun yi amfani da jirgi mara matuƙi sun ga duk abin da ke faruwa jiya Lahadi.

Mutumin ya shaida wa jaridar ta wayar tarho cewa galibin mutanen garin sun arce zuwa cikin jeji har da shi domin tsira da rayuwarsu.

A wani faifan bidiyo da aka naɗa lokacin da jirage marasa matuƙa ke shawagi a garin ranar Lahadi, an ji wani matashi na kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki.

Sojoji sun tarwatsa mutane a Okuama

Majiyar ta ce:

"Yanzu da nake magana da ku, sojoji da wasu matasa sun kutsa kai cikin garin, sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sun ajiye jiragensu a Okoloba sannan suka ƙariso a ƙafa."

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun mamaye ofishin SERAP awanni bayan kungiyar ta nemi a binciki NNPCL

"Sun bankawa tantunan da muka haɗa wuta, don me sojoji za su haɗa kai da maƙiyanmu su kawo mana hari? An kama shugabanniu a makonnin baya yanzu kuma sun zo su tarwatsa mana gari."

Sai dai majiyar ba ta bayyana musabbabin wannan sabon samame da sojoji suka kai garin Okuama ba.

Ogun: Matasa sun yi wa soja taron dangi

A wani rahoton kuma wasu fusattatun matasa sun cinna wuta ga wani mutum da suka zarga da hannu wajen sace babur da ake sana'ar acaba.

Bayan kashe mutumin, an ji cewa matasan sun yi wa wani soja rauni sosai, suka nemi hallaka shi kafin ya tsallake rijiya ta baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262