Duk da Tsige Shi daga Sarauta, Sanatan APC Ya ba Gwamna Shawara kan Talakawa
- Sanata Shehu Umar Buba ya yi kira ga gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed kan rabawa mutane tallafin gwamnatin tarayya
- Shehu Umar Buba ya ce gwamnatin tarayya ta ware kudi N3bn domin rabawa wadanda suka shiga jarrabawar ambaliyar ruwa a Bauchi
- Haka zalika Sanatan ya raba kudi da kayan tallafi ga wadanda suka shiga jarrabawar ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Shehu Umar Buba ya yi kira na musamman ga gwamnan jihar Bauchi.
Sanata Shehu ya bukaci gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da ya gaggauta karbar kudi da gwamnatin tarayya ta ware ga jihar.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sanata Shehu ya ce an ware kudi Naira biliyan uku domin tallafawa al'ummar jihar Bauchi.
An ware N3bn ga jihar Bauchi
Sanata Shehu Umar Buba ya ce gwamnatin tarayya ta ware kudi N3bn ga jihar Bauchi domin tallafawa wadanda suka yi fama da ambaliyar ruwa.
Shehu Umar Buba ya yi kira ga gwamnan jihar Bauchi da ya gaggauta karbar kudin da raba shi ga al'ummar jihar.
Shehu: 'A raba kudin yadda ya kamata'
Sanata Shehu Umar Buba ya yi kira ga gwamna Bala Muhammad kan tabbatar da raba kudin ga wadanda abin ya shafa.
Ya ce kudin zai rage raɗaɗi ga al'ummar jihar da suka yi fama da ambaliyar ruwa a damunar bana.
Sanata Shehu ya raba tallafi a Bauchi
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Shehu Umar Buba ya raba tallafin kudi N10m da buhunan shinkafa 500.
An tabbatar da cewa za a raba kayan tallafin ne a ƙananan hukumomin Darazo, Katagum, Jama'are, Zaki da Giade.
An sauke Sanata daga sarauta a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu ya sauke Sanata Shehu Buba Umar daga sarautar Majidaɗin Bauchi.
Majalisar masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne bisa zargin Sanata Shehu Buba Umar da rashin mutunta Gwamna Bala Mohammed.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng