Ana Kukan Tsadar Litar Fetur, Gwamnati Ta Warware Batun Karin Harajin VAT
- Gwamnatin Bola Tinubu ta musanta cewa ta bayyana cewa ba ta yi karin harajin VAT ga 'yan kasar nan zuwa 10% ba
- An samu rahotannin fargabar kara farashin VAT daga 7.5% da aka karba a kan kayayyakin da ake sayarwa a kasar nan
- Ministan tattalin arziki ya bayyana cewa gwamnati ba za ta karya doka ta fara karbar 10% na harajin VAT haka kawai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya karyata rahotannin da ke cewa an kara harajin VAT zuwa 10% daga 7.5%.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa, Ministan ya tabbatar da cewa harajin na VAT yana nan a 7.5% kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin haraji.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Wale Edun ya ce don haka gwamnatin tarayya ko wata hukumar ba ta da damar da za ta yi wani abu da ya saba dokokin harajin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta karyata karin harajin VAT
Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya ce jita-jitar da wasu kafafen yada labarai ke yadawa kan batun harajin VAT da jawo wa yan kasa wahala ba gaskiya ba ne.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Mista Edun ya kara da gwamnati na kokarin saukakawa ‘yan kasa da ‘yan kasuwa ta hanyoyi da dama.
"An janye harajin wasu kaya," Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta bayar da umarnin dakatar da harajin shigo da kayayyaki daga kasashen waje saboda rage wahala ga 'yan kasar nan.
Ministan tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka, inda ya lissafa wasu daga cikin kayan da cewa sun hada da shinkafa, alkama da wake.
An zuga shugaba Tinubu ya kara haraji
A baya kun ji cewa shahararren mai kudi a duniya, Bill Gates ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba ta karbar haraji yadda ya kamata, inda ya ce haraji na taimakawa wajen ayyukan kasa.
Bill Gates ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kawo kasar nan, inda ya ke jawabin a daidai lokacin da ake shawartar gwamnatin Bola Tinubu ta kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10%.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng