Ajuri Ngelale: Kura Kurai 2 da Suka Jawo Hadimin Tinubu Ya Ajiye Aikinsa

Ajuri Ngelale: Kura Kurai 2 da Suka Jawo Hadimin Tinubu Ya Ajiye Aikinsa

  • Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi hutun da bai bayyana ranar dawowarsa ba a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba
  • Ko da yake, ya ce ya ajiye aikinsa ne domin kula da rashin lafiya, wani sabon rahoto ya bayyana cewa, ɗan jaridar ya daina samun ganin Shugaba Tinubu
  • Ajuri Ngelale wanda tsohon ɗan jarida ne kafin ya samu muƙamin a gwamnatin Tinubu ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ajuri Ngelale ya sanar da cewa ya ajiye aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Ajuri Ngelale ya bayyana cewa ya tafi hutu daga aikin na sa ne sakamakon rashin lafiyar iyalansa.

Kara karanta wannan

"Ba rashin lafiya ba ne": An fadi ainihin 'dalilin' Ajuri Ngelale na ajiye aikinsa

Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa
Wasu na ganin Tinubu korar Ajuri Ngelale ya yi Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Legit.ng ta fahimci cewa lallai akwai matsalar rashin lafiya a cikin iyalinsa amma ba shine dalilin da ya sa ya yanke shawarar ya tafi hutun ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Ajuri Ngelale ya ajiye aiki?

A cewar rahoton jaridar The Cable, Ajuri ya hango cewa akwai yiwuwar a raba shi da kujerar shi yasa ya ɗauki matakin tafiya hutun.

Jaridar ta bayyana cewa Ngelale ba ya samun damar ganin Shugaba Bola Tinubu.

"An buƙaci Ajuri ya zaɓi tsakanin zama kakakin shugaban kasa ko jakadan sauyin yanayi. Yace a bari ya yi tunani a kai. Ya dawo ya zaɓi mai magana da yawun shugaban ƙasa amma an gaya masa cewa za a sanya masa ido domin a fili yake yana buƙatar taimako."

- Wata majiya a Villa

Kura-kuran Ajuri Ngelale

An sha gayawa Tinubu “taimakon” da ya ke buƙata wanda wasu daga cikinsu sun hada da kura-kurai a cikin sanarwar da yake fitarwa ga manema labarai

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: Tinubu ya yi magana bayan hadiminsa ya ajiye aiki, ya dauki mataki

Na farko, ya yi kuskure ya sanar a watan Satumba na 2023 cewa Tinubu shine shugaban ƙasa a Afirka na farko da ya buga ƙararrawa a Nasdaq.

Na biyu, ya yi gaggawar sanar da matakin da gwamnatin ƙasar hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta ɗauka na dage takunkumin hana biza ga ƴan Najeriya.

Shehu Sani ya magantu kan ajiye aikin Ngelale

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi magana bayan murabus din hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale.

Tsohon Sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya ce a yanzu ne Ajuri Ngelale zai ɗan samu ya yi kiba saboda hutun da zai yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng