Sheikh Gumi Ya Fadi Dalilin 'Yan Bindiga na Daukar Makamai

Sheikh Gumi Ya Fadi Dalilin 'Yan Bindiga na Daukar Makamai

  • Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya sake fitowa ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Arewacin Najeriya
  • Sheikh Gumi ya yi fatali da zargin da wasu ke yi kan cewa ƴan siyasa ne ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga suna kai hare-hare
  • Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa ƴan bindiga suna yaƙi ne saboda yadda aka yi watsi da su ba tare da ilmi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan matsalar ƴan bindiga da ake fama da ita.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa ƴan siyasa ba sa ɗaukar nauyin tashe-tashen hankula a yankin Arewacin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro, sun cinnawa ofishin 'yan sanda wuta

Gumi ya yi magana kan 'yan bindiga
Sheikh Gumi ya fadi abin da 'yan bindiga suke so Hoto: Dr Ahmed Mahmud Gumi
Asali: Facebook

A wata hira da jaridar The Punch, Sheikh Gumi ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa ƴan siyasa ne ke haddasa tashe tashen hankula a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sheikh Gumi ya ce kan ƴan bindiga

Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa ƴan bindiga sun ɗauki makamai ne saboda yadda aka yi watsi da su ba tare da ba su ilmi ba.

"Wannan zargi ne mara hankali. Babu wani ɗan siyasa da ke ɗaukar nauyin waɗannan mutane. Mu duka abin ya shafa. Ƴan adawa ba su ba ne suke ɗaukar nauyin su."
"Wannan abin da suke yi martani ne kan watsi da aka yi da su na tsawon lokaci ba tare da ilmi ba."
"Yanzu sun san inda duniya ta dosa kuma suna son ilmi. Mutanen nan sun san yanar gizo kuma suna ganin irin yadda aka mayar da su koma baya. Suna son su yaƙi hakan, wannan ba wani ya sanya su ba."

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi martani mai zafi kan harin 'yan ta'adda a Yobe

- Sheikh Ahmad Gumi

Gumi ya magantu kan kisan Sarkin Gobir

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan kisan sarkin Gobir.

Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci a sake shiri sosai a Najeriya domin kawo karshen ta'addanci da ya hana mutane sakat.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng