Gwamna Ya Ɗauki Zafi kan Yan Bindiga, Ya Bukaci Malamai Su Faɗi Sakon Manzon Allah
- Malam Dikko Umaru Radɗa ya buƙaci mutanen Katsina su tashi su kare mutuncin su da na iyalansu daga hare-haren ƴann bindiga
- Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci malamai su isar da saƙon Allah da Manzonsa game da matakin da ya kamata mutane su ɗauka kan ɓarayi
- Radda ya ce gara mutuwa da mutum ya tsaya a gabansa wasu ƙatti su kwanta da matarsa da ɗiyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina -Gwamn Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina su dauki matakan kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ya yi wannan kiran ne a wata ziyara da ya kai shiyyar Daura domin tattaunawa da al'umma kan abubuwan da suke bukatar gwamnati ta yi a kasafin kuɗin 2025.
Gwamna ya roki malamai su faɗar da mutane
Daily Trust ta ce Radda ya bukaci malaman addinin Musulunci da su fadakar da mutane game da muhimmancin kare kai kamar yadda Musulunci ya tanada.
Gwamnan, wanda ya nuna damuwarsa a fili, ya ce abin takaici ne wasu tsirarun ƴan bindiga su shiga gari guda, amma mutane su bari su ci mutuncinsu.
A cewarsa, bai dace a ce busassun ƴan bindiga uku da yunwa ta masu katutu za su tasa mutum 1,000 ba yayin da sauran jama'a ke jin tsoro wasu su ɓoye a karƙashin gado.
Gwamna Raɗɗa ya bukaci a kare kai
"Ga malamanmu a nan, ya zama dole a kansu su isar da saƙon Manzon Allah (SAW) game da ɓarayon da ya zo farautar rayuwarka ko dukiya. Me Allah ya ce ka yi?"
"Wane irin lalacewa ce ka tsaya kana kallo wasu su yi amfani da matarka da ɗiyarka? Ina amfanin rayuwarka? Gara mutuwa da irin wannan wulaƙancin."
"Suna tsoron kauyukan da suka san mutane na tunkararsu, ba su zuwa waɗannan kauyukan, don haka dole mu tashi tsaye mu dakatar da kashe-kashen da ake mana, mu zauna cikin shiri."
- Dikko Radda.
Yadda mutane za su tari ƴan bindiga
Gwamnan ya ce idan ƴan bindiga 5 zuwa 10 suka shiga gari, matukar mutane 500 za su haɗu su tunkare su, to kafin ɗayansu ya kashe mutum 5 an murƙushe shi, Daily Post ta kawo.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Gwamna Radda ya yi wannan kiran na mutane su kare kansu ba, ko a watan Fabrairu ya yi irin wannan kira.
Wani matashin Malami a yankin karamar hukumar Ɗanja, Malam Yahuza Bn Abdalla ya ce kalaman gwamna suna da tushe a Musulunci.
Malamin ya shaidawa Legit Hausa cewa:
"Duk wanda ya mutu wajen kare mutunci kansa, iyalansa da dukiyarsa ana sa ran ya yi shahada kamar yadda Manzon Allah SAW ya faɗa, saboda haka gaskiya gwamna ya faɗa.
"Bai kamata mutane su tsaya ana masu wani cin mutuncin ba, amma tsoro ya yi mana yawa, kowa tsoron mutuwa yake. Sai dai tambaya ɗaya zan yi wa shugabanni, shin sun sauke nauyin da ke kansu?
Dikko zai fara biyan sabon albashi
A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka cimma matsaya da NLC.
Dikko Umaru Radda ne ya sanar da haka kuma ya ce jihar Katsina za ta kasance a gaba gaba kan maganar ƙarin albashin ma'aikata
Asali: Legit.ng