Ministocin Buhari 5 da EFCC, ICPC, Suka Taso a gaba da Bincike da Aka Bar Ofis
Abuja - Akwai wasu da suka rike mukaman ministoci a gwamnatin Mai girma Muhammadu Buhari da yanzu ake taso da bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A rahoton nan, jaridar Legit Hausa ta kawo wasu cikin tsofaffin ministocin da hukumomin ICPC ko EFCC su ke fama da su a Najeriya.
Ministocin Muhammadu Buhari da ake bincike
1. Sadiya Umar Farouk
Kwanakin baya an ta jin yadda hukumar EFCC ta ke binciken Sadiyar Umar Farouk wanda ta kasance ministar jin kai da walwalar jama’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da kan ta, Sadiyar Umar Farouk ta tabbatar a X cewa an gayyace ta domin amsa tambayoyi game da badakalar N37.1bn lokacin tana ofis.
2. Hadi Sirika
Hadi Abubakar Sirika da ‘danuwansa da wasu kamfanoni biyu sun gamu da binciken hukumar EFCC bayan ya bar kujerar ministan tarayya.
Hukumar ta EFCC ta ce ana tuhumar tsohon Ministan harkokin jirgin saman da laifuffuka 10 da suka shafi badakalar biliyoyin kwangila.
3. Abubakar Malami
Bayan ya bar matsayin Ministan shari’a, The Cable ta ce an soma binciken Abubakar Malami kan wasu abubuwa da suka faru lokacin mulki.
Zargin biyan $496m ga kamfanin GSHL, shari’ar Paris Club, badakalar Abacha da aikin Mambilla sun jawo tsokano matsala da jami’an EFCC.
4. Saleh Mamman
A baya aka rahoto cewa EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman a gaban kotun tarayya a Abuja kan zargin N33.8bn da yake minista.
Premium Times ta ce a karshe alkali ya bukaci a tsare tsohon ministan makamashin a gidan gyaran hali da ke Kuje a garin Abuja.
5. Chris Ngige
Kwanan nan kuma aka ji hukumar ICPC ta biyo ta kan Sanata Chris Ngige wanda ya yi ministan kwadago a gwamnatin da ta gabata.
Ana zargin Chris Ngige da laifi wajen ba da kwangila a hukumar NSITF lokacin da yake ofis, ya yi kusan shekaru takwas yana minista.
Ana bukatar Tinubu ya nada Ministoci
Duk da akwai Ministoci sama da 40, ku na da labari cewa a yanzu jihar Filato ba ta da ko Minista guda a majalisar zartarwa (FEC).
An yi wata da watanni babu Ministar jin kai a Najeriya a sakamakon dakatar da Betta Edu da aka yi a Junairu domin a bincike ta.
Asali: Legit.ng