Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Gaskiya kan Halin da Ake Ciki a Kasa
- Fasto Adewale Giwa na jihar Ondo ya fito fili ya soki salon mulkin shugaban ƙasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
- Faston ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu sun jefa al'ummar Najeriya cikin wahala
- Ya caccaki shugaban ƙasan kan nuna rashin tausayin halin da ƴan Najeriya suke ciki inda yake yin abubuwa kamar ana mulkin soja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Babban fasto na cocin Awaiting the Second Coming of Jesus Christ Ministry, Adewale Giwa, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu.
Adewale Giwa ya buƙaci Bola Tinubu ya daina yi kamar ƙasar nan na ƙarƙashin mulkin soja.
Malamin addinin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Akure, babban birnin jihar Ondo, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya caccaki Bola Tinubu
Adewale Giwa ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu sun jefa ƴan Najeriya cikin wahala.
"Shugaba Tinubu yana son ya yi amfani da shekara biyu na gwamnatinsa wajen amfanar da ƴan uwa da abokan arziƙinsa tare da yin amfani da sauran shekara biyun wajen amfanar da wasu tsirarun ƴan Najeriya."
"Na hango wannan wahala za ta zo, tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
"Na gargaɗi al’umma cewa gwamnatin da ke kan mulki yanzu sai ta fi ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari taɓarɓarewa."
"Abin da zan iya cewa shi ne, muna buƙatar rahamar Allah da ya fitar da mu daga ƙangin da muke ciki.
"Wannan gwamnatin tana yin abubuwa ne kamar Najeriya tana ƙarƙashin mulkin soja. Shugaban ƙasa bai nuna tausayi, bai nuna cewa ba ya jin daɗin abin da yake yi."
- Fasto Adewale Giwa
An buƙaci Tinubu ya kori ministoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Ibrahim Modibbo, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori da yawa daga cikin ministocinsa.
Ibrahim Modibbo wanda tsohon daraktan yaɗa labarai ne na Nuhu Ribadu, ya nuna cewa shekara uku ne kacal suka ragewa Tinubu ya sauya akalar gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng