'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Harin Ta'addanci a Katsina

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Harin Ta'addanci a Katsina

  • Ƴan bindiga sun kai wani harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina a yankin Arewa maso Yamma
  • Miyagun ƴan bindigan sun raunata jami'an tsaro mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutum uku zuwa cikin daji
  • Jibia da ke a bakin iyakar Najeriya da Nijar na daga cikin ƙananan hukumomi masu fama da matsalar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Aƙalla mutane uku ne suka samu munanan raunuka yayin da ƴan bindiga suka kai hari a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutum uku a harin da suka kai a garin Magama na ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun sace mutane a Katsina Hoto: @Miqdad_jnr
Asali: Twitter

Wani 'dan kwamitin tsaro na Jibia ya shaidawa tashar Channels tv a ranar Alhamis cewa ƴan bindigan sun yi galaba a kan jami’an tsaron da aka tura domin fatattakar su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro, sun cinnawa ofishin 'yan sanda wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11:45 a daren ranar Laraba, inda suka rika harbe-harbe domin tsorata mazauna yankin waɗanda galibinsu ke shirin kwanciya barci.

"Ƴan bindigan sun zo da yawansu inda suka kai farmaki a Magama. Sun harbi mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutum uku."

- Mamba a kwamitin tsaro

Legit Hausa ta tuntuɓi mataimakin kwamitin tsaro na Jibia, Malam Nasiru Jibia wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Malam Nasiru ya bayyana cewa jami'an tsaron da aka raunata ƴan banga ne waɗanda suka fita domin fatattakar ƴan bindigan.

"Eh sun kawo harin da daddare amma mutanen mu sun samu nasarar fatattakarsu. Sai dai sun sace mutum uku tare da raunata ƴan banga mutum uku."

- Malam Nasiru Jibia

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi martani mai zafi kan harin 'yan ta'adda a Yobe

An cafke mai siyan kayan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun kama wani mutum da ake zargin yana siyan kayan sata daga ƴan bindiga da ke garkuwa da mutane a jihar Katsina.

Wanda ake zargin mai suna Malam Lawal Jikan Dada ya tabbatar da cewa yana harkokin kasuwanci da miyagun ƴan bindigan da suka addabi bayin Allah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng