Kifar da Tinubu: Baturen da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Fadi Dalilin Kin Mika Kansa

Kifar da Tinubu: Baturen da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Fadi Dalilin Kin Mika Kansa

  • Andrew Wynne wanda rundunar ƴan sandan Najeriya ke nema ruwa a jallo ya yi magana kan dalilinsa na ƙin miƙa kansa
  • Baturen ɗan ƙasar Ingila ya bayyana cewa yana tsoron ya rasa ransa a hannun ƴan sanda shiyasa ya ƙi dawowa kasar nan
  • Mista Andrew Wynne bayyana cewa idan ya dawo Najeriya da wuya ya kai ƙarshen shekarar nan yana numfashi a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Baturen nan da rundunar ƴan sandan Najeriya ke nemansa ruwa a jallo, Andrew Wynne, ya ce ba zai miƙa kansa ga hukumomi ba.

Andrew Wynne ya ce ba zai miƙa kansa ga ƴan sanda ba saboda yana tsoron ya rasa ransa a hannunsu.

Kara karanta wannan

Kifar da Tinubu: Ƴan sanda sun mayar da martani kan ikirarin Baturen da ake nema

'Yan sanda na neman bature ruwa a jallo
Andrew Wynne ya ce yana tsoron rayuwarsa Hoto: @DejiAdesogan/Nigeria Police Force
Asali: UGC

A yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Laraba, Andrew Wynne, ya ce ba zai rayu ba idan ya miƙa kansa ga ƴan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Andrew ba zai miƙa kansa ba?

Andrew Wynne ya bayyana cewa wani ma'aikacinsa mai suna, Yomi, wanda ƴan sanda suka cafke shi ya fuskanci azabtarwa mai tsanani.

Ya bayyana cewa ba zai yarda ya bari irin hakan ya faru da shi ba.

Andrew Wynne mai shekara 70 a duniya ya bayyana cewa idan ya miƙa kansa ga ƴan sanda, kafin ƙarshen shekarar nan sai ya bar duniya.

"Ƴan sanda sun bayyana cewa idan ina da gaskiya na miƙa kai na. Ina da gaskiya. Misali kamar Yomi, ba shi da laifi kuma ya miƙa kansa amma an azabtar da shi."
"Hakan akwai tsoro ko babu? Yomi yaro na ne kuma ba shi da laifi amma an azabtar da shi har na tsawon kwanaki uku."

Kara karanta wannan

"Ka bi a hankali": Gwamnan PDP ya gargadi kwamishinan 'yan sanda

"Kuma ƴan sanda suna tsammanin na dawo Najeriya domin su azabtar da ni? Tsoro na shi ne ba zan rayu ba. Ba batun jin tsoron azabtarwa ba ne, batun tsoron rayuwata ne. Ba na tunanin zan rayu zuwa ƙarshen shekarar nan idan na dawo Najeriya."

- Andrew Wynne

Ƴan sanda sun magantu kan Andrew Wynne

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta buƙaci ɗan ƙasar Burtaniya da ake nema ruwa a jallo, Andrew Wynne, da ya fito daga inda yake ɓoye ya mika kansa.

Ƴan sanda sun kuma musanta ikirarin Wynne cewa ba a gayyace shi ba kafin a ayyana shi a matsayin wanda ake nema.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng