Sanata a Arewa Ya Duba Halin da Ake Ciki, Ya Bayar da Tallafin Tirela 200 Na Abinci
- Sanata Abdul'aziz Yari ya bayar da tallafin tirelar masara 200 domin a rabawa mabuƙata a lungu da saƙo na jihar Zamfara
- Tsohon gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne da nufin sauke farashin kayan abinci a kasuwa da taimakawa marasa ƙarfi
- Kwamitin da aka kafa domin raba wannan tallafi ya ce sama da mutum 200,000 za su amfana a faɗin kananan hukumomin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Sanata Abdul'aziz Yari (APC, Zamfara ta Yamma) ya ƙara ba da tallafin tireloli 200 na masara domin a rabawa mutane a lungu da saƙon jihar Zamfara.
Mai magana da yawun kwamitin rabon tallafin, Ibrahim Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce sabon tallafin da tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ya bayar ya zo a daidai lokacin da jama’a ke matukar bukatar abinci, Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim ya ce kwamitin raba tallafin ƙarƙashin jagorancin Hon Lawal M Liman (Gabdon Kaura) ya gana da kwamitocin kananan hukumomi a Gusau ranar Laraba.
Zamfara: Yadda aka tsara raba tallafin Yari
A jawabin da ya yi a wurin taron, shugaban kwamitin Lawal M Liman ya ce kowace ɗaya daga ƙananan hukumomin Gummi da Talata Mafara za ta samu tirela 20.
Ya ƙara da cewa sauran ƙananan hukumomi 11 za su samu tirela 12 da za a rabawa maɓukata da masu ƙaramin karfi daga Sanata Abdul'aziz Yari.
Shugaban kwamitin ya yi bayanin cewa a tsarin da suka yi na rabon tallafin, akalla mutane 230,400 ake sa ran za su ci gajiya, rahoton Vanguard.
Dalilin Yari na ƙara bada tallafi a Zamfara
Hon. Lawal M Liman ya ce ambaliyar ruwan da aka yi kwanan nan a Gummi da kuma tsadar kayan abinci a kasuwa na cikin dalilan da suka ja hankalin Abdul'aziz Yari ya ware tallafin.
A cewarsa, tsohon gwamnan ya aiko da tirela 200 na masara a rabawa talakawa da niyyar rage masu raɗaɗi da kuma sauke farashin kayan abinci.
Sanata Yari ga ba ƴan Najeriya shawara
A wani rahoton kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara ya buƙaci ƴan Najeriya su dage da yi wa Bola Tinubu addu'a a kokarinsa na tabbatar da tsaro a ƙasar nan.
Sanata Abdul'aziz Yari ya ce duk wasu matakai da ya kamata, tuni gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka saura kawai addu'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng