Kano: Ambaliya Ta Halaka Mutum 31, Gidaje 5,280 Sun Rushe a Kananan Hukumomi 21

Kano: Ambaliya Ta Halaka Mutum 31, Gidaje 5,280 Sun Rushe a Kananan Hukumomi 21

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta ce akalla mutane 31 ne suka rasu sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwa
  • Shugaban hukumar Isyaku Kubarachi ya ce ambaliyar ta shafi mutane sama da 30,000 a kananan hukumomi 21
  • Ya ce gwamnati na kokarin yadda za a samar da kayan tallafi domin ragewa waɗanda ambaliyar ta rutsa da su raɗadi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ibtila'in ambaliyar ruwa ya yi sanadin rasuwar mutum 31 tare da lalata gidaje 5,280 a ƙananan hukumomi 21 na jihar Kano.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta Kano (SEMA), Isyaku Kubarachi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ƴan jarida ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ambaliya ta yi ajalin mutane 31 tare da lalata dubban gidaje a jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yadda ambaliya ta yi ɓarna a Kano

Daily Trust ta rahoto Isyaku Kubarachi na cewa ambaliyar ta shafi mutane akalla 31,818, sannan ta lalata amfanin gonakin jama'a da suka kai kimanin 2,518.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mutane 31,818 ne ambaliyar ta shafa, ta ruguza gidaje 5,280 tare da lalata gonaki 2,518, kimanin kadada 976, sannan an samu asarar rayuka aƙalla 31.”

Shugaban SEMA ya kara da cewa ambaliyar ta auku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a kusan ko'ina a jihar Kano.

Kazalika ya ce galibin gidajen da ruwan ya ruguza na ƙasa ne kuma an gina su a kan hanyar ruwa.

Isyaku ya ce da farko an yi hasashen ambaliyar za ta faru ne a ƙananan hukumomi 14.

Amma a karshe ambaliyar ta shafi 21 ciki har da Wudil, Gwale, Nassarawa, Dala, Tarauni, Dawakin-Tofa, Dambatta da sauransu.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun hallaka babban hadimin shugaban majalisa a Najeriya

Gwammatin Kano za ta tallafawa mutane

Ya ce hukumar SEMA ta miƙa shawarwari ga gwamnatin Kano domin duba yadda za a tallafawa magidantan da ibtila'in ya shafa.

"Gwamnati na kokarin yadda za a samar da kayan agaji ga kananan hukumomi 21 da ambaliyar ta shafa, kuma nan bada jimawa ba za a turo kayan.
"A yanzu dai waɗanda ambaliyar ta raba da muhallansu sun koma gidajen ƴan uwa da zama," in ji shugaban SEMA.

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano

A wani rahoton zanga zangar adawa da karin kudin mai ta barke a jihar Kano awanni bayan da kamfanin man fetur na Najeriya ya sanar da karin kudin.

An rahoto cewa daruruwan masu sana’ar adaidaita sahu suka mamaye titunan Kano domin nuna fushinsu kan karin kudin da aka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel