Yadda Ake Zargin Yunwa Na Kashe Fursunoni a Gidajen Yarin Najeriya
- Ana zargin cewa yunwa tana yin illa ga mutanen da aka daure saboda laifuffuka daban daban a gidajen gyaran halin Najeriya
- Wani babban 'dan jarida da ke ketare ya bayyana yadda wasu ma'aikatan gidajen gyaran hali suka nuna yadda ake rayuwa a kaso
- Ya bayyana kudin da ake warewa kowane dan fursuna a rana domin cin abinci amma kuma ya yi zargin hakan bai samuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Ana zargin cewa yunwa na yin barazana ga rayuwar yan Najeriya da aka kulle a gidajen gyaran hali.
An ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara kudin abinci da ake kashewa domin ciyar da yan fursuna a watan Agusta.
Legit ta tatttaro bayanan da Jafar Jafar ya fada ne a cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin mutuwar yan fursunan Najeriya
Jafar Jafar ya rubuta cewa yan fursuna da dama na fama da bakar wahala a gidajen gyaran halin Najeriya.
Dan jaridar ya kawo labarai daga gidajen yari da dama inda ma'ikata suka shaida cewa wasu yan fursuna na mutuwa wasu kuma suna ta ramewa saboda yunwa.
Lamarin yana faruwa ne yayin da yunwa ke kara tsananta a Najeriya saboda tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke fuskanta.
Kuɗin abincin 'yan fursuna a Najeriya
'Dan jaridar da yanzu ya samu mafaka a Landan ya ce a baya ana ware N750 ne domin ciyar da kowane dan fursuna sau uku a rana.
Sai dai ya ce a watan Agustan da ya wuce shugaba Bola Tinubu ya mayar da kudin zuwa N1,125 amma a haka kudin ke lalacewa hannun 'yan kwangilar abinci.
Dan jaridar ya yi zargin cewa yan fursunan ba su ga kokarin da Bola Tinubu ya yi a kan lamarin ba har yanzu inda ya bukaci a tsananta bincike.
Obasanjo: 'Yan siyasa sun cancanci dauri'
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce ya kamata 'yan siyasa da shugabanni su kasance a daure.
Obasanjo ya ce mafi yawansu ba su da tarbiyya ko halayya na kwarai saboda ba gyaran kasa ba ne a gabansu idan suka samu mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng