Kotu Ta Ba da Belin Dan Jaridar da Ya Soki Abba da Sanusi II, Ta Kafa Sharudda

Kotu Ta Ba da Belin Dan Jaridar da Ya Soki Abba da Sanusi II, Ta Kafa Sharudda

  • Wata kotun majistare da ke zamanta a birnin Kano, ta ba da belin ɗan jaridar da aka tsare a gidan gyaran hali kan sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ɗan jaridar mai suna Mukhtar Dahiru an tura shi gida gyaran hali bayan ƴan sanda sun cafke shi kan sukar gwamnan da Sarki Muhammadu Sanusi II
  • Kotun ta ba da belin ɗan jaridar kan kuɗi N1m tare da gindaya masa sharaɗin kawo mutum uku da za su tsaya masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kotu ta bayar da belin wani ɗan jarida aka tsare a gidan gyaran hali kan sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Sarakunan Kudancin Najeriya sun yi magana kan kisan Sarkin Gobir, sun ba gwamnati shawara

Ɗan jaridar mai suna Mukhtar Dahiru, wanda ma'aikacin gidan Rediyo Najeriya ne da ke aiki a Pyramid FM Kano, jami'an ƴan sanda ne suka cafke shi sannan aka tsare shi a gidan gyaran hali.

Kotu ta ba da belin dan jarida a Kano
Kotu ta ba da belin dan jaridar da aka tsare kan sukar Gwamna Abba da Sanusi II Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sukar Abba, Sanusi: Ɗan jarida ya samu beli

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wata kotun majistare da ke zamanta a Kano ta bayar da belin ɗan jaridar a ranar Talata, 3 ga watan Satumban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Ummah Kurawa, ta ba da belin Mukhtar Dahiru a kan kuɗi N1m tare da hana shi yin rubutu a soshiyal midiya wanda zai iya zama cin fuska ga jami'an gwamnatin jihar, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Wane sharuɗɗa aka gindaya masa?

Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da kawo mutum uku da za su tsaya masa, wanda dole ne ɗaya daga cikinsu ya kasance shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ).

Kara karanta wannan

Kifar da Tinubu: Ƴan sanda sun mayar da martani kan ikirarin Baturen da ake nema

Sauran su ne matarsa da wani amintaccen mutum wanda hukumar Hisbah ta yarda da shi.

Daga nan sai kotun ta ɗage zaman har zuwa ranar, 2 ga watan Oktoban 2024 domin ci gaba da sauraron shari'ar.

An gurfanar da hadimin tsohon Gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta gurfanar da hadimin Sanata Aminu Tambuwal kan cin zarafin gwamna.

Ana zargin Shafi'u Tureta da cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu inda ya wallafa wani faifan bidiyo da cewa bai iya yaren Turanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng