"Ka da ka Zama El Rufai": An ba Uba Sani Shawara Bayan Rattaba Hannu da Kamfanin China

"Ka da ka Zama El Rufai": An ba Uba Sani Shawara Bayan Rattaba Hannu da Kamfanin China

  • Ƙungiyar matasan kiristocin Arewa (NCYP) ta yi magana kan yarjejeniyar da Gwamna Uba Sani ya cimmawa da kamfanin Huawei
  • Ƙungiyar NCYP ta buƙaci gwamnan da ya guji maimaita irin kura-kuran da gwamnatin magabacinsa, Nasir El-Rufai ta yi a Kaduna
  • Shugaban NCYP a wata sanarwa ya yaba da yarjejeniyar da gwamnan ya cimmawa da kamfanin inda ya ce za ta kawo ci gaba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar matasan kiristocin Arewa (NCYP), ta ba gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani shawara.

Ƙungiyar NCYP ta buƙaci Gwamna Uba Sani ya guji tafka irin kura-kuran da magabacinsa Nasir El-Rufai ya yi a yayin da yake ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyin ƙasashen waje a madadin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun fusata da kalaman Wike, sun hada shi da jami'an tsaro

An ba Gwamna Uba Sani shawara
Kungiyar NCYP ta ba Uba Sani shawara Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

An yabawa Gwamna Uba Sani

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NCYP, Isaac Abrak, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban NCYP ya yabawa gwamnan bisa rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Huawei na ƙasar China.

Isaac Abrak ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata gagarumar nasara da za ta iya inganta ɓangaren ICT na jihar da kuma samar da sababbin damammaki ga matasa.

"El-Rufai ya bar Kaduna da bashi", NCYP

Ya yi tsokaci kan gwamnatin El-Rufai da ta karɓo lamunin $350m daga bankin duniya domin bunƙasa ilimi wanda daga ƙarshe ba a cimma manufar da ta sanya aka karɓo shi ba.

"Muna kira ga gwamnati da ta guji yin irin kura-kuran da aka yi a baya, musamman waɗanda aka yi a gwamnatin da ta shuɗe ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai da ta ci bashin $350m domin bunƙasa harkar ilmi."

Kara karanta wannan

"Ka bi a hankali": Gwamnan PDP ya gargadi kwamishinan 'yan sanda

"Abin takaici ba a cimma manufar wannan bashin ba, sannan a yau an bar mutanen jihar Kaduna da nauyin biyan bashin da bai amfanar da komai ba."

- Isaac Abrak

El-Rufai ya caccaki shugabanni

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa, hassada ce ta yi katutu a zukatan da yawa daga manyan ƴan siyasan Najeriya.

A bayanin da ya yi, ya yi fashin baki ne ga yadda siyasar Amurka take da kuma yadda Joe Biden ya hakura ya mika tikitin takara ga abokiyar takararsa Kamala Haris.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng