Tofa: Ƴan Sanda Sun Bayyana Bature da Ya Nemi Kifar da Gwamnatin Tinubu a Najeriya

Tofa: Ƴan Sanda Sun Bayyana Bature da Ya Nemi Kifar da Gwamnatin Tinubu a Najeriya

  • Ƴan sandan Najeriya sun ayyana neman 'dan kasar Burtaniya bisa zargin kitsa yadda za a kifar da gwamnatin Bola Tinubu
  • Mai magana da yawun ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da haka yayin hira da ƴan jarida a hedkwata da ke Abuja
  • Ya ce bayan bincike mai zurfi, jami'an tsaro sun kama mutum bakwai da ake zargin da bada gudummuwar kuɗi a zanga-zangar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ayyana Andrew Wynne, ɗan ƙasar Burtaniya wanda aka fi sani da Andrew Povich a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Ƴan sanda suna neman baturen wanda ɗan asalin kasar Burtaniya ne bisa zargin ƙulla-kulla da ƴunkurin kifar da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Sabuwar zanga zanga ta ɓarke a Abuja, matasa sun aika sako ga Shugaba Tinubu

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
To fa: ƴan sanda sun bayyana wanda ya yi ƙoƙarin kifar da Gwamnatin Tinubu a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, shi ne ya sanar da haka a hedkwatar ƴan sanda da ke Abuja yau Litinin, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun gano makircin da aka ƙulla

Ya ce Baturen ya karɓi hayar wani shago tare da buɗe wurin sayar da litattafai, sannan ya buɗe wata makaranta duk domin ɓoye shirinsa na yiwa Najeriya zagon ƙasa.

Adejobi ya ce shaidun fili da na ɓoye sun tabbatar da cewa wanda ake zargin ya riƙa bibiyar zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, 2024, rahoton Punch.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa sun gano baturen ya ba da maƙudan kuɗi da dabarun yadda masu zanga-zangar za su kifar da zaɓabbiyar gwamnati.

Jami'an yan sanda sun kama mutum 7

"Rundunar ƴan sanda ta gudanar da bincike mai zurfi kan zargin wasu ƴan ƙasashen ƙetare da ɓata gari sun yi yunƙurin kifar da zababbiyar gwamnati a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a wani farmaki a jihar Sokoto

"Bayan tattara bayanan sirri tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro, an kama mutum tara da aka turo masu kudi daga waje domin su ruguza Najeriya."
"A masaniyar farko mun gano cewa sun kitsa makirci tare da ba da tallafin kudi ga zanga-zangar da aka yi domin tayar da tarzoma da canza gwamnati ta haramtacciyar hanya."

- Olumuyiwa Adejobi.

Masu zanga-zanga sun kai ƙara kotu

A wani rahoton kuma masu zanga-zangar da aka kama a Najeriya sun kai ƙara kotu kan umarnin tsare su na tsawon kwanaki 60.

Mutanen waɗanda suka haɗa da ƙananan yara sun aika saƙo ga Bola Tonubu, inda suka ce ba shi hurumin ɗaukar mataki a kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262