Fasinjoji da Dama Sun Bace yayin da Jirgi Ya Kife a Bauchi

Fasinjoji da Dama Sun Bace yayin da Jirgi Ya Kife a Bauchi

  • Wani jirgin Kwale-Kwale ya samu hatsari a jihar Bauchi inda wasu mutum uku suka ɓace ba a san inda suka yi ba
  • Hatsarin jirgin dai ya auku ne a kogin Zindiwa da ke ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi a ranar Asabar, 31 ga watan Agustan 2024
  • Masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutum bakwai daga cikin fasinjoji 10 da hatsarin jirgin ya ritsa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - An samu aukuwar wani hatsarin jirgin Kwale-Kwale a jihar Bauchi.

Hatsarin jirgin kwalwe-kwalen ya auku ne a ranar Asabar a kogin Zindiwa, dake ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.

Jirgin ruwa ya kife a Bauchi
Jirgin kwale kwale ya yi hatsari a Bauchi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda hatsarin jirgin ya auku?

A cewar rahoton jaridar The Punch, hatsarin ya yi sanadiyyar ɓacewar mutane uku yayin da aka samu nasarar ceto wasu mutum bakwai.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 10,000 a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jirgin mai ɗauke da fasinjoji 10 ya kife ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a lokacin da yake ƙoƙarin tsallaka kogin Zindiwa.

An dai yi amfani da jirgin ne a matsayin hanyar sufuri sakamakon ambaliyar ruwa da ta katse babban titin, lamarin da ya tilastawa mazauna wurin komawa amfani da kwale-kwale domin isa wuraren da suke.

Tawagar ceto daga wani ƙauye da ke kusa sun kawo ɗauki cikin gaggawa, inda suka yi nasarar ceto fasinjoji bakwai, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da aukuwar lamarin,

Kakakin ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin, inda ya ƙara da cewa mutane biyu sun ɓace yayin da aka samu nasarar ceto fasinjoji uku.

Kara karanta wannan

"Zan kunno muku wuta a jihohinku," Ministan Tinubu ya yiwa wasu gwamnoni barazana

Mutane sun rasu a hatsarin jirgi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutane biyar sun rasa rayukansu yayin da wani Kwae-kwale ya kife a garin Ganta da ke karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.

Kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji da dama ya gamu da haɗari ne a yammacin jiya Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng