An Shiga Jimami Bayan Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama da 10,000 a Jihar Arewa

An Shiga Jimami Bayan Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama da 10,000 a Jihar Arewa

  • An samu ambaliyar ruwan da ta raba da mutane sama da 10,000 a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Ambaliyar ruwan ta auku ne a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar bayan an samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya
  • Gwamnan jihar wanda ya ziyarci inda abin ya shafa, ya bayar da tallafi tare da alƙawarin gyara hanyoyin ruwa da samar da sababbi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Sama da mutane 10,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da gonaki da wasu kadarori na miliyoyin naira suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Zamfara.

An samu ambaliyar ruwan ne bayan da aka shafe makonni ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Fasinjoji da dama sun bace yayin da jirgi ya kife a Bauchu

An samu ambaliyar ruwa a Zamfara
Ambaliyar ruwa ta raba mutane da gidajensu a Zamfara Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Getty Images

Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a Zamfara

Sarkin Gummi, Mai shari’a Hassan Lawal (mai ritaya) ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a lokacin da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya kai ziyarar gani da ido a ƙaramar hukumar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci garin Gummi da al'ummar Gayari a ranar Asabar domin duba irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.

Da yake yiwa gwamnan jawabi, mai shari’a Hassan Lawal ya bayyana yadda al’amura suka kasance a ƙaramar hukumar.

"Bayan tattaunawar da muka yi da masana, da alama za a iya samun mafita ta dindindin. Bisa abin da muka duba, gidaje 10,291 ne abin ya shafa amma mun fahimci cewa gwamnan zai zagaya domin gani da kansa."

- Mai shari'a Hassan Lawal

Gwamna Dauda ya ba da tallafi

A nasa ɓangaren, gwamnan ya jajantawa waɗanda ambaliyar ta shafa, sannan ya sanar da bayar da agajin gaggawa na Naira 100,000 tare da raba buhunan hatsi 10,000 da gidajen sauro da barguna ga mutanen, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamna ya ba da tallafin kudi da filaye ga wadanda ambaliya ta shafa

Gwamna Dauda Lawal ya kuma yi alƙawarin magance matsalar ambaliyar ruwa ta hanyar gina sababbin magudanan ruwa, gyara madatsun ruwa da gina sababbin madatsun ruwa.

Tinubu ya yi alhinin ambaliyar ruwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya nuna alhininsa ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya ce ya ƙudiri aniyar bayar da tallafin da ya dace domin ganin sun farfaɗo daga asarar da suka yi sakamakon ambaliyar ruwan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng