Abba Ya Sa Tsoho Sharba Kuka a Gidan Gwamnati, Allah Ya Amsa Addu’ar Dattijo

Abba Ya Sa Tsoho Sharba Kuka a Gidan Gwamnati, Allah Ya Amsa Addu’ar Dattijo

  • Mai girma Abba Kabir Yusuf ya ci karo da tsohon da aka gani a bidiyo yana neman a taimaka masa
  • Hakar wannan mutumi ta cin ma ruwa, domin gwamna ya ba shi kyautar N1m kuma za a ba shi abinci
  • Gwamnan jihar Kano bai tsaya a nan ba, za a nemo gida a saya masa domin ya huta da tozarcin haya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Wani tsoho da aka ji ya fito kwanaki yana neman taimakon Mai girma gwamnan jihar Kano, ya samu abin da yake so.

A wancan lokaci an ji wannan bawan Allah ya roki Abba Kabir Yusuf ya taimaka masa domin kuwa yana neman matsuguni.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taimakawa tsoho a Kano Hoto: Salisu Muhammad Kosawa
Asali: Facebook

Tsoho ya hadu da Gwamna Abba Yusuf

Kara karanta wannan

"Hassada ta yiwa 'yan siyasar Najeriya katutu": El-Rufai ya caccaki masu fada a ji a Najeriya

Yau Asabar, 31 ga watan Agusta 2023, sai ga bidiyon ganawar tsohon da gwamna a shafin Malam Salisu Yahaya Umar a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da Hadimin na Abba Kabir Yusuf ya wallafa, an ga wannan dattijo yana kuka saboda farin cikin da gwamna ya sa shi.

Lokacin da bidiyonsa ya fara yawo a shafukan sada zumunta, an ji na kusa da gwamnati suna cigiyar inda za a samu mutumin.

Yadda Abba ya taimakawa dattijo

Kamar yadda tashar Freedom ta rahoto, gwamna ya taimakawa dattijon da N1m kuma ya yi alkawarin saya masa gida mai kyau.

Ibrahim Adam ya bayyana cewa Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi umarni a ba masoyin na shi kayan abinci, zai huta da cefane.

Da yake zantawa da gwamnan, dattijon ya shaida cewa a unguwar Gwammaja yake zama inda mutane suka rika yi masa dariya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

An ji Abba Kabir ya yi bayanin tasiri Gwammaja a tafiyar Kwankwasiyya, yake cewa ita ce unguwar Marigayi Malam Aminu Kano.

Soyayyar tsohon da Kwankwasiyya

Dattijon wanda masoyin Kwankwasiyya ne ya ce bai da kudi kuma bai da ‘ya ‘ya ko jikoki saboda haka ne aka nemi a tozarta shi.

Mutane sun ba tsohon shawarar ya tuntubi Sanata Barau Jibrin, amma sai ya ce babu abin da zai sa ya rabu da gidan Kwankwasiyya.

Gwamnatin Abba za ta yaki saida filaye

Kuna da labari cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai sa kafar wando daya da masu taba filayen gwamnati suna cefanarwa.

Abba ya ce a sanar da gwamnati idan an ga wani asibiti, makaranta, makabarta, masallaci ko wajen shakatawar al'ummar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng