“Hassada Ta Yiwa ’Yan Siyasar Najeriya Katutu”: El-Rufai Ya Caccaki Masu Fada a Ji a Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana matsayarsa kan yadda siyasar Amurka ke tafiya daidai ba tare da tangarda ba
- Malam Nasir El-Rufai ya ce, tabbas akwai hassada da keta da ke tattare da ‘yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa masu fada a ji
- Tun bayan sauka daga kujerar gwamna ake kai ruwa rana tsakanin Nasir da kuma magajinsa Sanata Uba Sani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa, hassada ce ta yi katutu a zukatan da yawa daga manyan ‘yan siyasan Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter (X) a ranar Asabar 31 ga watan Agustan 2024.
Wannan sako na El-Rufai dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tuhumarsa kan zargin cinye wasu kudade da ake alakantawa da gwamnatin jihar ta Kaduna inda ya kasance gwamna na tsawon shekaru takwas.
Dalilin kiran ‘yan siyasan Najeriya da mahassada
A bayanin da ya yi, ya yi fashin baki ne ga yadda siyasar Amurka take da kuma yadda Joe Biden ya hakura ya mika tikitin takara ga abokiyar takararsa Kamala Haris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakon nasa, ya ce tabbas hassada ke kaiwa ga kiyayya, wacce daga baya ke zama babbar matsala da rasa komai.
Hakazalika, ya yi mamaki tare da dasa ayar tambayar cewa, yaushe ne hassada mai girma zuwa kiyayya za ta kau a zukatan ‘yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa masu fada a ji.
Yadda aka fara zargin El-Rufai
Tun bayan saukarsa a mulki a jihar Kaduna ake kai ruwa rana tsakanin tsohon gwamnan da kuma gwamna mai ci a yanzu, Sanata Uba Sani.
An zargi Malam Nasir da amfani da kudaden gwamnatin Kaduna ta hanyoyin da ake zargin ya azurta kansa ne da makusantansa.
Sai dai, El-Rufai ya sha musanta zargin da ake masa a lokuta mabambanta tare da bayyana shirinsa na wanke kansa a kowanne lokaci.
Batun El-Rufai kan zargin lamushe wasu kudade
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan hassada tsakanin yan siyasa.
El-Rufai ya fadi haka ne a daidai lokacin da ake zargin gwamnatinsa da almundahana da dukiyar al'umma.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.
Asali: Legit.ng