Masu Zanga Zangar da Aka Kama Sun Fusata, Sun Tura Zazzafan Saƙo ga Tinubu

Masu Zanga Zangar da Aka Kama Sun Fusata, Sun Tura Zazzafan Saƙo ga Tinubu

  • Masu zanga-zangar da aka kama a Najeriya sun kai ƙara kotu kan umarnin tsare su na tsawon kwanaki 60
  • Matasan waɗanda suka haɗa da ƙananan yara sun aika saƙo ga Bola Tonubu, inda suka ce ba shi hurumin ɗaukar mataki a kansu
  • Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da bukatar rundunar ƴan sanda na ci gaba da tsare waɗanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Matasan da jami'an tsaron Najeriya suka cafke a lokacin zanga-zangar yunwa sun yi fatali da umarnin kotu na ci gaba da tsare su.

Sun shaidawa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu cewa ba shi da hurumin kama su, musamman saboda yana daya daga cikin wadanda suka fi amfana zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Katsina: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin ƙarshe kan kujarar ɗan majalisar tarayya

Tinubu da masu zanga zanga.
Masu zanga-zangar da aka kama sun kalubalanci umarnin tsare su na watanni 2 a gaban kotu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Masu zanga-zangar sun shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1233/2024, suna kalubalantar hukuncin babbar kotun tarayya, kamar yadda Punch ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta amince a tsare masu zanga-zanga

Idan zaku iya tunawa kotun ta umarci rundunar ƴan sanda ta ci gaba da tsare matasan na tsawon watanni biyu domin gudanar da bincike.

Masu zanga-zangar sun kalubalanci wannan hukunci a ƙarar da suka shigar, inda suka ambaci babban sifetan ƴan sanda na kasa a matsayin wanda suke ƙara.

Tun farko dai matasan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a mafi yawan jihohin ƙasar nan tsakanin 1-10 ga watan Agusta, suka nuna fushinsu kan tsadar rayuwa.

Wace kara masu zanga-zangar suka shigar?

Masu karar sun shaidawa kotu a takardar ƙara cewa ana kokarin tauye masu haƙƙi da kuma jirkita gaskiya ne shiyasa aka nemi ci gaba da tsare su.

Kara karanta wannan

Yara 'yan kasa da shekara 18 sun tafi kurkuku kan 'yunkurin' kifar da gwamnati

A cewar masu zanga zangar ta hannun lauyansu, Femi Falana (SAN) gurfanar da su da aka yi gaban ƙuliya don neman izinin tsare su ya saɓawa doka, Vanguard ta tattaro.

Bisa wannan ne suka nemi kotu ta soke tare da jingine hukuncin tsare su na kwanaki 60, sannan ta wanke su daga zargi domin a sake su, su koma cikin iyalansu.

Gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye bayan zanga-zanga

A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zanga-zangar da aka yi ta ƙara tunatar da ita bukatar yawan sauraron koken jama'a.

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa ya ce a yanzu gwamnati na zama ta saurari koken ƴan Najeriya fiye da a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262