An Yi Gumurzu: Matasa Sun Kwace Bindiga Sun Harbi Jami’an NDLEA
- Rahotanni da suka fito daga Bayelsa sun yi nuni da cewa wasu matasa sun tare jami'an hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi
- An ruwaito cewa bata garin matasan sun kwace bindigar da wani jami'in NDLEA yake rike da ita kuma suka harbi jami'an
- Shugaban hukumar NDLEA a jihar Bayelsa, Kanu Chukwuemeka ya tura zazzafan gargaɗi ga dukkan mutanen yankin da abin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bayelsa - Hukumar yaki da safara da shan miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi gargadi bayan an kwace bindiga a hannun jami'anta.
Wasu matasa bata gari ne suka kwace bindigar a yankin Oruma a jihar Bayelsa daga hannun jami'an NDLEA.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa bayan kwace bindigar, matasan sun yi barna ga jami'an NDLEA din.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matasa suka kwace bindigar hukuma
Kakakin hukumar NDLEA a jihar Bayelsa, Daniel Howells Obah ya ce wasu matasa a yankin Oruma sun toshe wata gada da jami'an NDLEA suka zo wucewa.
Biyo bayan toshe gadar sai suka nuna yawa ga jami'an NDLEA din suka kwace bindiga ƙirar Pistol wacce aka lodawa harsashi.
Barnar da matasa suka yiwa NDLEA
Bayan sun kwace bindigar, matasan sun kubutar da wasu masu laifi guda biyu da aka kama kuma sun lalata motar jami'an NDLEA.
Daɗin dadawa, Danil Howells Obah ya ce matasan sun harbi jami'an NDLEA tare da jiwa wasu raunuka.
Matasan sun tsere ne yayin da suka hango sauran jami'an NDLEA sun tunkaro wajen da abin ya faru.
Shugaban NDLEA ya yi gardagi a Bayelsa
Tribune ta wallafa cewa shugaban NDLEA a jihar Bayelsa, Kanu Chukwuemeka ya ba mutanen yankin wa'adin kwanaki bakwai su fito da bindigar ko su hadu da fushin hukuma.
Kanu Chukwuemeka ya yi kira ga shugabannin yankin kan su tabbatar da cewa sun fito da bindigar da sauran mutane biyun da aka ƙubutar.
NDLEA za ta fara gaji ga dalibai
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) za ta rika yi wa dalibai masu neman shiga manyan makarantu gwaji.
Ana sa ran gwajin zai taimaka wajen gano dalibai masu ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma taimaka masu da wasu dabarun samun sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng