'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin 'Yan Bindiga Na Sace Mutane a Katsina

'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin 'Yan Bindiga Na Sace Mutane a Katsina

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta reshen jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin da ƴan bindiga kuka kai
  • Jami'an ƴan sandan sun daƙile harin ne a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar da ke yankin Arewa maso Yamman Najeriya
  • Ƴan sandan tare haɗin gwiwar ƴan banga sun fatattaki ƴan bindigan, aka ceto wata yarinya da aka yi yunƙurin sacewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasara kan miyagun ƴan bindiga yayin wani hari da suka kai a jihar.

Jami'an rundunar ƴan sandan sun yi nasarar daƙile yunƙurin da wasu ƴan bindiga suka yi na yin garkuwa da wata yarinya a ƙauyen Faru da ke ƙaramar hukumar Jibia a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun hallaka jami'in tsaro, ,sun sace manoma

'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanya a shafin X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan sandan Katsina suka daƙile harin

A cewar ASP Abubakar ƴan sandan sun yi nasarar daƙile harin ne a daren ranar Alhamis, 29 ga watan Agustan 2024.

"Da misalin ƙarfe 1:15 na dare, an samu kiran gaggawa a ofishin ƴan sanda na Jibia, kan harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Faru, ƙaramar hukumar Jibia, inda suka yi garkuwa da mutum ɗaya."
"Nan take DPO na Jibia ya haɗa tawagar jami'ai tare da haɗin gwiwar rundunar KSWC da ƴan banga inda suka garzaya domin kai ɗauki ƙauyen."
"Jami'an tsaron sun yi musayar wuta da ƴan bindigan, inda suka yi nasarar ceto yarinyar da aka yi garkuwa da ita ba tare da ta ji rauni ba, tare da daƙile harin yayin da maharan suka tsere ɗauke da raunukan bindiga daban-daban."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 1 tare da sace wasu mutane a Nasarawa

- ASP Abubakar Sadiq

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun harbe wani ɗan banga mai suna Saleh Aliyu a Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma.

Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu manoma huɗu a ƙauyen Nasarawar Azzara kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng