Mai Shara Ya Tsinci $10, 000 a Jirgin Sama, Ya Maida Kudin da Sun Haura N16m

Mai Shara Ya Tsinci $10, 000 a Jirgin Sama, Ya Maida Kudin da Sun Haura N16m

  • Har yanzu akwai sauran masu tsoron Allah, wani mai shara ya mayar da $10,000 da ya tsinta lokacin da ya ke aikinsa
  • Mai sharar, Auwal Ahmed Dankode ya tsinci dalolin Amurka da kudinsu ya kai Naira Miliyan 16 a kudin Nairar Najeriya
  • Auwalu, wanda dan asalin karamar hukumar Bunkure ne a jihar Kano ya mayar da kudin da ya tsinta jirgin Egypt Air

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wani mai aikin shara a filin jirgin Malam Aminu Kano, Auwal Ahmed Dankode ya mayar da dalolin da ya tsinta a lokacin da ya ke tsaka da gudanar da aikinsa.

Kara karanta wannan

Kasuwancin Arewa zai habaka, tashar tsandaurin Kebbi ta bude ofishi a Kano

Matashin ya tsinci $10,000 wanda ya kai Naira Miliyan 16 a kudin Najeriya, ya tsinci kudin a cikin jirgin Egypt Air a lokacin da ya ke share cikinsa.

Matashi
Matashi ya mayar da $10,000 da ya tsinta a Kano Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Auwal Ahmed Dankode dan asalin karamar hukumar Bunkure ne a jihar Kano wanda ke yiwa kamfanin Nigeria Aviation Handling Company aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai $10,000 ya zo neman kudinsa

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Auwal bai jima da mayar da $10,000 da ya tsinta ba wani bawan Allah - balarabe ya taho neman wasu kudi da ya rasa.

Bayan balaraben ya sha tambayoyi ne aka tabbatar da cewa kudin na sa ne, domin ya zo daidai da lambar kujerar da aka tsinci kudin a wajen.

Wanda ya tsinci $10,000 ya magantu

Matashin da ya tsinci dalolin Amurka lokacin da ya ke aiki a Kano, Auwal Ahmad Dankode ya bayyana farin cikinsa bisa yadda mai kudin ya rika murna.

Kara karanta wannan

Kwara: Ana cikin halin kunci, dattijuwa mai shekara 54 ta haifi jarirai 11, miji ya kidime

Ya ce ya ji dadi sosai ta yadda Allah SWT ya yi amfani da shi wajen sanya farin ciki a tattare da wani, inda ya ce matakin da ya dauka shi ne daidai.

Matashi ya mayar da kudin tsintuwa

A baya kun ji cewa wani matashin mai tuka baburin adaidaita sahu a Kano ya tsince wata bakar jaka makare da kudi, sannan ya mika ta ga jami'an rundunar 'yan sanda a jihar.

Matashin mai suna Safiyanu Mohammed ya tsinci kudin a kwanar Dakata lokacin da ya ke aiki, kuma kakakin rundunar yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sa cigiyar mai jakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.