Daga Karshe Shugaban NLC Ya Hallara Ofishin 'Yan Sanda, an Samu Bayanai
- Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero ya hallara a ofishin tawagar ƴan sanda ta IRT da ke birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis
- Ajaero ya je ofishin ne domin amsa gayyatar da jami'an tsaron suka yi masa bisa zargin da ake yi masa na ɗaukar nauyin ta'addanci da wasu laifuffuka
- Shugaban na NLC ya samu rakiyar lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana zuwa ofishin na ƴan sanda domin amsa tambayoyin da za a jefa masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) Kwamared Joe Ajaero, ya amsa gayyatar da ƴan sanda suka yi masa.
Kwamred Joe Ajaero ya hallara a ofishin tawagar ƴan sanda ta IRT da ke a tsohuwar Abattoir kusa da kwanar Guzape a birnin Abuja.
Joe Ajaero ya isa wajen ƴan sanda
Jaridar The Nation ta rahoto cewa a tare da Ajaero akwai lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana SAN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun isa ofishin ne da misalin ƙarfe 10:20 na safe domin amsa gayyatar da ƴan sanda suka yi masa bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da wasu laifuffuka.
Tun da farko dai ƙungiyar ƙwadago ta yi kira ga mambobinta da su yi gangami domin yi wa Joe Ajaero rakiya zuwa ofishin na ƴan sanda.
'Yan kungiyar NLC sun yi gangami
Sai dai, Femi Falana ya gayawa ma'aikatan da su tsaya a hedkwatar NLC domin gudun yin hatsaniya a wajen ƴan sandan, rahoton da jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya ba da tabbacin cewa lauyoyin da ke cikin tawagarsa za su kula da komai yadda ya kamata.
Yayin da ma'aikata na ƙungiyoyi da dama suke zaman jira a hedkwatar NLC, an kawo jami'an ƴan sanda wurin.
Dalilin samamen ƴan sanda a hedkwatar NLC
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun bi sahun wani wanda ake zargi zuwa wani shago a ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC).
Kakakin rundunar ƴan sandan, Muyiwa Adejobi bayyana cewa an gudanar da aikin ne domin cafke wani ɗan kasar waje da ke da hannu wajen aikata laifuka da dama a faɗin Najeriya da sauran ƙasashen Afirika.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng