Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari, Fasinjoji Sun Mutu Gaba Ɗaya a Arewa
- Wani kwale-kwale da ya ɗauko mutum biyar ya nutse a garin Ganta da ke ƙaramar hukumar Buji a jihar Jigawa
- Rahotanni daga mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da ruwa ya ci ƙarfin jirgin, duka fasinjojin sun rasu
- Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Jigawa, ya ce duk da koƙarin da aka yi ba a samu nasarar ceto mutanen a raye ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigawa - Mutane biyar sun rasa rayukansu yayin da wani Kwae-kwale ya kife a garin Ganta da ke karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.
Kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji da dama ya gamu da haɗari ne a yammacin jiya Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.
Jigawa: Yadda kwale-kwalen ya nutse
Rahoton Leadership ya nuna cewa Kwale-kwalen ya gamu da ruwa mai ƙarfi a daidai a wani yanki da aka yi ambaliyar ruwa da ke kusa da garin Ganta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan lamari dai shi ne karo na uku da aka yi hatsarin kwale-kwale a jihar Jigawa da ke Arewa maso Yamma a daminar bana.
Rahotanni sun bayyana cewa dukkan fasinjoji biyar da kwale-kwalen ya ɗauko sun mutu a ruwan sakamakon haɗarin jiya Talata.
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa igiyar ruwa ce ta ci ƙarfin kwale-kwalen, nan ya fara tangal-tangal daga bisani ya nutse a ruwan.
Ƴan sanda suka kai ɗaukin gaggawa
Kakakin ƴan sandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari.
Ya ce mutanen yankin da suka iya ruwa da ‘yan sanda sun yi bakin kokarinsu wajen ciro gawarwakin fasinjojin.
Lawal Shiisu ya kara da cewa wadanda haɗarin ya rutsa da su sun hada da mata biyu da maza uku daga Malamawar Gangara da ke karamar hukumar Birnin Kudu.
Jigawa: Yadda aka yi koƙarin ceto su
"Bayan samun rahoton, take tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sarkin ruwa da mutanensa suka garzaya wurin da nufin ceto su da ransu,” in ji Lawan.
Sai dai duk da hanzarin kai ɗauki, Lawal ya ce daga baya jami’an lafiya a asibitin Ganta Cottage sun tabbatar da mutuwar fasinjojin, rahoton Sahara Reporters.
Wani mazaunin Birnin Kudu a Jigawa, Habib Abdullahi ya koka kan rayukan da aka rasa a Jigawa a daminar bana.
Magidancin ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa ambaliya da haɗarin kwale-kwale ya ci rayukan mutane da dama a sassan Jigawa.
"Rasa rayukan da aka yi bana ya fi na kowace shekara, akwai waɗanda na sani da suka rasu sakamakon ambaliya, muna fatan Allah ya karɓi shahadarsu.
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta nan Jigawa su ɗauki matakan da suka dace domin kare afkuwar waɗannan bala'o'i nan gaba," in ji shi.
Badaru ya bada tallafi a Jigawa
A wani labarin kuma ministan tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru ya tuna da al'ummar da annobar ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Jigawa.
Badaru ya ba da tallafin N20m ga gwamnatin jihar domin taimaka mata a ƙoƙarin da take yi na tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng