Yayin da Ambaliya ke Rusa Gidajen Kaduna, Gwamnatin Uba Sani Za Ta Gina Sabon Birni
- Gwamnatin Kaduna da haɗin gwiwar Urban Shelter na shirin gina sabon birni a kan fili mai girman kadada 200
- Gwamnatin Uba Sani za ta samar da gidajen ne domin saukakawa jama'a wajen mallakar muhalli mai inganci
- Da ya ke kaddamar da aikin, Uba Sani ya ce shirin samar da gidajen na daga cikin kokarin magance karancin muhalli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na magance matsalar karancin muhalli da wasu mazauna jihar ke fuskanta.
Gwamna Uba Sani ne ya bayyana haka yayin kaddamar da gina gidaje a New Millennium City da gwamnati ke yi da hadin gwiwar Urban Shelter.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da babban mai ba gwamna Uba Sani shawara kan kafafen yada labarai na zamani, Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin kaddamar da aikin gidajen, gwamnan wanda ya samu wakilcin matamaiyarsa, Dr. Hadiza Balarabe ya ce an yi haka ne domin saukakawa talakawa.
Za a gina gidaje 5000 a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta gina gidaje masu sauki guda 500 a sassan jihar domin jama'a su samu gidaje masu sauki da inganci
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr. Hadiza Balarabe ce ta bayyana haka, inda ta ce za a gina gidaje masu sauki 5000 a fadin jihar, Jaridar Punch ta wallafa.
Kaduna: Za a gina wasu gidaje 200
Gwamnatin Uba Sani ta ce za ta gina gidaje masu sauki guda 200 a yankin Kamazou da ke karamar hukumar Chikun.
Za a sayarwa jama'a gidajen a farashi mai rahusa domin sama masu muhalli mai inganci.
Gwamnati za ta gina sababbin birane
A baya kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na shirin gina sabon birni a Kano, inda aka fara biyan diyyar wadanda aikin zai bi ta gonakinsu a Dawakin Kudu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a gina biranen ne domin rage cunkoso daga cikin gari, yayin da za a kara gina wasu gidajen a Unguwar Rimi da Lambu a Dawakin Kudu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng