Gwammatin Tinubu Ta Gano Matar da Ta Yi Barazanar Kashe Ƴan Najeriya a Kasar Kanada
- Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar NiDCOM ta gano bayanan matar nan da aka ji tana yi wa ƴan Najeriya barazana a kasar Kanada
- A wani faifan bidiyo da ya watsu a X, an ji matar tana cewa za ta fara amfani da abinci da abin sha mai guba wajen kashe yarbawa
- Shugabar hukumar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce tuni masu kishin ƙasa da ke zaune a Kanada suka fara koƙarin ɗaukar mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwammatin tarayya ta gano suna da bayanan matar nan mazauniyar ƙasar Kanada, wacce ta yi barazanar kashe ƴan uwanta ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasar.
A wani faifan bidiyo da ya bazu a manhajar X, an ji matar tana kalaman ɓatanci da nuna ƙin jinin yarbawa ƴan asalin Najeriya.
Wace barazana matar ta yiwa 'yan Najeriya?
Kamar yadda The Nation ta rahoto, matar ta yi iƙirarin zubawa yarbawa guba a abinci kuma ita ma ta ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ku ji da kyau, lokaci ya yi da zamu fara kashe yarbawa, za mu zuba masu guba a abinci da abin sha," in ji ta
Matar ta kuma sha alwashin cewa za ta riƙa zuwa wurin aiki da abubuwa masu guba, sannan ta baiwa duk wani bayerabe da ɗan kasar Benin da ta haɗu da shi.
Ta kuma bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne domin martani kan ƙiyayyar da ake nunawa Igbo.
Matar ta ce tana zaune ne a birnin Ontario na kasar Canada, kuma duk wanda ya ga zai iya, ya kai ta ƙara gaban hukumomin kasar.
Gwamnatin Najeriya ta gano bayanan matar
Shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna kasashen ketare (NiDCOM) Abike Dabiri-Erewa ta ce sun gano sunan matar, Amaka Patience Sunnberger.
Da take karin haske kan lamarin ranar Laraba, 28 ga watan Agusta, shugabar NiDCOM ta ce:
"Wannan ne hoton matar da ta yi wannan ɓaɓatun, sunanta Amaka Patience Sunnberger, ta goge shafinta na TikTok kua yanzu haka ƴan Najeeiya sun kai ƙorafinta ga mahukunta a Kanada."
LP ta shirya taron masu ruwa da tsaki
A wani rahoton na daban Mista Peter Obi da Gwamna Alex Otti sun kira taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar LP karo na farko bayan zaɓen 2023.
Mai magana da yawun gwamnan Abia, Dodoh Okafor ya ce za a gudanar da taron ranar 4 ga watan Satumba, 2024 a gidan gwamnati da ke Umuahia.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng