Ana Rade Radin Barinsa APC, Gwamna Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa

Ana Rade Radin Barinsa APC, Gwamna Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa

  • Gwamnan jr Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya naɗa sababbin manyan sakatarori guda 12 a ma'aikatun gwamnatin jihar
  • Shugaban ma'aikatan jihar, Elijah Evinemi ne ya tabbatar da amincewar da gwamnan ya yi domin naɗa sababbin manyan sakatarorin a cikin wata sanarwa
  • Elijah Evinemi wanda ya taya murna kan muƙaman da suka samu ya buƙace su da yi aiki tuƙuru domin sauke nauyin da ke wuyansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo, ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori guda 12 a ma’aikatun jihar.

Gwamna Ododo ya naɗa sababbin manyan sakatarorin ne domin cike guraben da ake da su.

Gwamna Ododo ya yi nade nade a Kogi
Gwamna Ododo ya nada manyan sakatarori Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Gwamna Ahmad Ododo ya yi naɗe-naɗe

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Mista Elijah Evinemi ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ododo ya jaddada cewa an zaɓo sakatarorin ne a tsanake bisa cancanta da adalci.

Yayin da yake taya su murnar nasarar da suka samu, shugaban ma’aikatan, Mista Elijah Evinemi, ya buƙaci sababbin manyan sakatarorin da su yi aiki tuƙuru.

Ya kuma buƙace su da su gudanar da ayyukansu cikin aminci, sadaukarwa, da riƙon amana, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Jerin sunayen waɗanda aka naɗa

Sababbin manyan sakatarorin sun haɗa da:

  • Momoh Aziz Steven, ƙaramar hukumar Ajaokuta.
  • Negedu Muhammed Bala, mazaɓar Ankpa 1.
  • Haruna Jibo Muhammed, ƙaramar hukumar Bassa.
  • Ejigbo Akoji, mazaɓar Dekina-Biraidu.
  • Enimola Enimola, ƙaramar hukumar Kabba-Bunu.
  • Fashoba Ayo-Lahadi, ƙaramar hukumar Mopa-Amuro.
  • Adurodija Ebenezer, ƙaramar hukumar Ogori- Magongo.
  • Enehe Dorcas Omeneke, ƙaramar hukumar Okehi.
  • Sanni Haruna Muhammed, mazaɓar Okene ta 1.
  • Ochu Philips Omeiza, mazaɓar Okene ta 11.
  • Shaibu Danjuma Fabian, ƙaramar hukumar Olamaboro.
  • Baiyegunsi S. Taiwo, ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

Gwamna Ododo ya yi murnar nasara a Kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kogi, ya yaba da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar sa a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana nasarar a matsayin hukuncin Allah maɗaukakin Sarki, inda ya buƙaci ƴan adawa da su zo a haɗa kai da su domin ciyar da jihar gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng