Rayukan Mutum 16 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Rayukan Mutum 16 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An rasa rayukan aƙalla mutane 16 a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Ore zuwa Ondo da daddare
  • Hatsarin wanda ya auku tsakanin wasu motoci guda biyu ya yi sanadiyyar ƙonewar mutum 16 yayin da wasu suka samu raunuka
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo ya tabbatar da aukuwar wannan hatsarin
  • Jami'in ya ce hadarin ya auku ne sakamakon gudun wuce gona da iri wanda aka dade ana gargadin direbobi a kan shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Aƙalla mutane 16 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a babbar hanyar Ore zuwa Ondo a jihar Ondo a daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun hallaka jami'in tsaro, ,sun sace manoma

Hatsarin wanda ya auku a ƙauyen Ajue da ke kan titin, ya haɗa da motoci biyu, wata motar bas ƙirar Toyota Hiace da wata babbar mota.

Mutane sun rasu a hatsarin mota a Ondo
An yi mummunan hatsarin mota a jihar Ondo Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Yadda hatsarin ya auku

Wata majiya ta shaidawa jaridar Leadership cewa mutane 16 sun ƙone, sannan wasu mutum uku sun samu munanan raunuka yayin da mutum biyu kuma suka tsira da rayukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar, musabbabin hatsarin shi ne taho mu gamar da motocin biyu suka yi sakamakon gudun da ya wuce gona da iri.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) na jihar, Ibitoye Samuel, ya ce hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Litinin, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

A cewar Ibitoye, ba a kammala bincike kan abin da ya haddasa hatsarin ba.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Ya ce binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya auku ne sakamakon gudun da ya wuce gona da iri.

Kwamandan na FRSC, ya buƙaci masu ababen hawa da su riƙa yin tuƙi cikin natsuwa da daina gudun da ya wuce gona da iri a kan hanya.

Mutane sun rasu a wani hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a lokacin da wani jirgin ruwa ya nutse a ƙauyen Okubie da ke ƙaramar hukumar Kudancin Ijaw a jihar Bayelsa.

Bayanai sun nuna cewa jirgin ruwan ya ɗauko fasinjoji 15 kuma ya gamu da hatsari ne a lokacin da ya keto da gudun da ake ganin ya wuce ƙima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng