'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kaduna, Sun Hallaka Jami'in Tsaro, Sun Sace Manoma

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kaduna, Sun Hallaka Jami'in Tsaro, Sun Sace Manoma

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai hari kan manoma a ƙauyen Nasarawar Azzara da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da manoma guda huɗu tare da hallaka wani ɗan banga lokacin da yake aiki a gonarsa
  • Wani shugaba a yankin da ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce sojoji sun cafke wani da ake zargin yana ba ƴan bindiga bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu miyagun ƴan bindiga sun harbe wani ɗan banga mai suna Saleh Aliyu a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu manoma huɗu a ƙauyen Nasarawar Azzara kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 1 tare da sace wasu mutane a Nasarawa

'Yan bindiga sun sace manoma a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka dan banga a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani shugaba a yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Asabar lokacin da ƴan bindigan suka farmaki manoman a hanyarsu ta zuwa gona.

Shugaban ya bayyana cewa kafin a kai wa manoman hari, ƴan bindigan sun harbe wani ɗan banga da ke aiki a gonar sa.

Sojoji sun kama wanda ake zargi

Ya kuma bayyana cewa sojoji sun kama wani da ake zargin mai ba ƴan bindiga bayanai ne a kasuwar ƙauyen a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Ya yi bayanin cewa bayan sojojin sun samu bayanan sirri sai suka bi sawun wanda ake zargin zuwa kasuwa inda ya je domin siyo kayan abinci da sauran kayayyaki ga ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi awon gaba da babban jami'in gwammati a Najeriya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ci tura.

Hakan ya faru ne saboda lokacin da aka neme shi a waya ba a same shi ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun kai hari a Nasarawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wani mutum mai suna Garba Yakubu a wani hari da suka kai a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutum biyu a yayin da suka kai harin a ƙauyen Gabaduke na ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng