Matasa Sun Taso Tinubu a Gaba Sai Ya Yi Murabus, Sun Fadi Dalili

Matasa Sun Taso Tinubu a Gaba Sai Ya Yi Murabus, Sun Fadi Dalili

  • Matasan ƙabilar Ijaw sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya haƙura da muƙaminsa na ministan man fetur na Najeriya
  • Matasan ƙarƙashin ƙungiyar Ijaw Youth Council (IYC) sun buƙaci shugaban ƙasan ya ba da muƙamin ga ƙwararrun masana a fannin
  • Sun bayyana cewa hankalin shugaban ƙasan ya rarrabu ta yadda ba zai iya gudanar da aikin yadda ya dace ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Matasan ƙabilar Ijaw a ƙarƙashin ƙungiyar Ijaw Youth Council (IYC), sun buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi murabus daga muƙamin ministan man fetur.

Matasan sun buƙaci Shugaba Tinubu ya naɗa tsayayyen wanda zai ci gaba da jagorantar ma'aikatar bayan ya yi murabus ɗin.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Yusuf Bichi, an bukaci babban jami'in gwamnati ya yi murabus

An bukaci Tinubu ya yi murabus
Kungiyar IYC ta bukaci Tinubu ya yi murabus daga mukamin ministan man fetur Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ƙungiyar IYC ta buƙaci Shugaba Tinubu ya yi murabus ne ta bakin kakakinta, Bedford Berefa, yayin wata tattaunawa da tashar News Central TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun buƙaci Tinubu ya yi murabus

A yayin tattaunawar wacce aka yi a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, kakakin na IYC ya ce ayyuka sun yiwa Tinubu yawa saboda haka ya kamata ya yi murabus daga muƙamin ministan man fetur.

"A matsayinsa na babban jami'in tsaro, Shugaba Tinubu yana da nauyin kare rayukan al'umma a wuyansa."
"A shekarar da ta gabata, mun samu matsalar ƙarancin man fetur biyo bayan cire tallafin mai da aka yi."
"Mun ga irin wahala da yunwar da hakan ya jawowa ƴan Najeriya. Hakan ya nuna cewa hankalin ministan man fetur, Shugaba Tinubu, ya rarrabu."
"Saboda haka, ya kamata ya haƙura da muƙaminsa na ministan man fetur. Ya kamata ya ba da wannan muƙamin ga ƙwararrun masana."

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun tono tsohon ƙulli game da alƙawarin Tinubu na biyan tallafin N25,000

- Bedford Berefa

An buƙaci ministan Tinubu ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi murabus daga kan muƙaminsa.

Wani babban mamba a jam'iyyar PDP, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, ya ba shugaban na kamfanin NNPCL shawarar ya ajiye aikinsa domin ya tsira da mutuncinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng