Nuhu Ribaɗu Ya Yi Babban Rashi, Allah Ya Yiwa Surukarsa Rasuwa a Abuja

Nuhu Ribaɗu Ya Yi Babban Rashi, Allah Ya Yiwa Surukarsa Rasuwa a Abuja

  • Dukkan mai rai mamaci ne, Allah ya yiwa, Hajiya Ummu Iya Abubakar, surukar Nuhu Ribadu rasuwa ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024
  • Iyalan marigayyar ne suka tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar, sun ce za a yi mata janaza a babban masallacin ƙasa da ke Abuja bayan Azahar
  • Sanarwar ta ƙara da rokon Allah ya gafartawa Hajiya Babba ya kuma sanya ta a gidan Aljannar Firdausi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya yi rashin surukarsa, Hajiya Ummu Iya Abubakar (Babba).

Hajiya Ummu ta riga mu gidan gaskiya ne da sanyin safiyar ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Malam Nuhu Ribadu.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ya yi rashi, surukar Malam Nuhu Ribaɗu ta rasu Hoto: Nuhu Ribaɗu
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da iyalan marigayyar suka fitar ta hannun Sanata (Farfesa) Iya Abubakar, kamar yadda Tribune Online ta ruwaoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta nuna cewa iyalan marigayyar sun shiga jimami da alhinin wannan rashi da suka yi ranar Talata.

Za a yi mata janaza a Abuja

Sun sanar da cewa za a gudanar da Sallar Janaiza da karfe 1:30 na rana bayan Sallar Zuhur a babban masallacin Abuja, sannan a binne ta a makabartar Gudu.

"A madadin Sanata Iya Abubakar da iyalai, cikin kanƙan da kai da mika wuya ga Allah SWT, muna sanar da rasuwar Hajiya Ummu Iya Abubakar (Babba)."
"Hajiya Babba ta koma ga mahaliccinta ne da sanyin safiyar yau Talata 27 ga watan Agusta 2024.
"Za a yi Sallar Janaza da misalin ƙarfe 1:30 na rana a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, daga nan za a kaita maƙabartar Gudu," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar surukar Ribadu: Atiku, Ganguje da wasu jiga jigan APC sun halarta

Sanarwar ta ƙara da rokon Allah ya gafarta mata, ya haɗa ta da kyawawan ayyukan da ta yi a tsayon rayuwarta.

"Allah SWT ya haɗa ta da ayyukanta na alheri, Ya gafarta mata zunubanta, Ya haskaka kabarinta, Ya sa ta a gidan Aljannah Firdausi. Ameen."

Yadda aka ƙashe ɗan sarki a Legas

A wani rahoton na daban rundunar yan sanda a jihar Legas ta fitar da bayani kan yadda yan bindiga suka kashe babban dan wani mai sarauta.

Yan bindigar sun kashe dan farin sarkin ne mai suna Tijjani Akinloye da tsakar rana kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262