Yajin Aiki: An Samu Matsala a Taron da Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi da ASUU
- An samu tsaiko a taron gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i ASUU wanda aka shirya gudanarwa ranar Litinin
- Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Okodeke ya tabbatar da haka, ana tsammani taron ya koma ranar Laraba mai zuwa
- Gwamnatin tarayya ta shirya zama da shugabannin kungiyar ASUU ne domin daƙile yunƙurin rufe jami'o'i a faɗin ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rahotannin da muka samu sun nuna cewa an ɗaga taron gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU).
Gwammatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta shirya taron ne yau Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024.
Kamar yadda The Nation ta rauwaito, gwamnati ta nemi zama da ASUU ne bayan ƙungiyar yi barazanar shiga yajin aiki cikin makonni uku idan ba a biya mata buƙatu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar ASUU ta ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da cewa an ɗage taron da za a yi yau Litinin.
Osodeke ya ce taron ba zai gudana ba kamar yadda ministan ilimi ya sanar ranar Jumu'a da ta gabata.
Yajin aiki: Meyasa aka ɗaga taron ASUU?
Duk da har yanzu ba a bayyana dalilin dage taron ba, amma a yanzu ana sa ran taron zai gudana a ranar Laraba 28 ga watan Agusta, 2024.
Idan ba ku manta ba a makon jiya, malaman jami'o'in gwamnati suka yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani kan abin da suka kira gaza cika alƙawarin gwamnati.
Dalilin ASUU na fara shirin yajin aiki
ASUU ta ce ta gaji da gafara sa bata ga ƙaho ba dagane da yarjejeniyar da aka cimmawa a shekarar 2009.
Ƙungiyar ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 21 ta yi abin da ya dace ko kuma ta rufe jamo'o'in gwamnati a faɗin ƙasar nan.
Bukatun ASUU dai sun haɗa da inganta walwala, ƙara kasafin jami'o'i da sauransu, rahoton Punch.
NLC na shirin tsunduma yajin aiki
A wani rahoton na daban, an ji kungiyar NLC karkashin Joe Ajaero ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashin wasu daga cikin mambobinta a bangaren ilimi.
Bayan warware takaddamar mafi karancin albashi a ranar Alhamis, kungiyar kwadago ta lashi takobin shiga yajin aikin gama gari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng