Shugaba Tinubu Ya Fadi Lokacin da 'Yan Najeriya Za Su Samu Sauki

Shugaba Tinubu Ya Fadi Lokacin da 'Yan Najeriya Za Su Samu Sauki

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun halin wuya da ƴan Najeriya ke fama da shi a halin yanzu a ƙasar nan
  • Shugaba Tinubu ya ce yana sane da cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri, amma za su haifar da ɗa mai ido
  • Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba manufofin gwamnatinsa da matakan da ya ɗauka za su samar da sauƙi ga ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri da nufin kawo sauƙi ga ƴan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba manufofinsa za su kawo sauki ga ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya juyawa Tinubu baya, ya fadi abin da zai sanya ya fadi zaben 2027

Tinubu ya sha sabon alwashi
Shugaba Tinubu ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya ɗauki alƙawari

Shugaban ƙasan ya kuma yi alƙawarin ci gaba da inganta tsarin doka, da bin ƙa'idojin raba madafun iko, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Lahadi a lokacin da ya buɗe babban taron ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) na shekara-shekara a Legas, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya aminta da tarihin ƙungiyar wajen fafutukar tabbatar da manufofin dimokuradiyya da inganta bin doka da oda.

Tinubu ya faɗi lokacin da sauƙi zai zo

Ya ba da tabbacin cewa duk ɗaukar matakai masu tsauro domin sauya yadda ake gudanar da abubuwa a baya zai samar da wahala, manufofin gwamnatinsa za su kawo sauƙi ga ƴan Najeriya nan ba da jimawa ba.

"Na aminta da cewa sauya yadda aka saba gudanar da abubuwa na buƙatar ɗaukar matakai masu tsauri, waɗanda ke zuwa da wahalhalu."

Kara karanta wannan

Kungiyar HURIWA ta bukaci Tinubu ya yi murabus, ta fadi dalili

"Sai dai, ina da ƙwarin gwiwar cewa wannan na wucin gadi ne sannan manufofinmu da ƙoƙarin da muke yi a matsayin gwamnati, za su kawo sauƙi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci."

- Bola Tinubu

Jigon APC ya hango rashin nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC kuma na hannun daman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan yiwuwar tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Cif Eze Chukwuemeka Eze ya bayyana cewa yunwar da ƴan Najeriya ke ciki ita za ta sanya su yi waje da Shugaba Tinubu daga kan kujerar mulkin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng