An Yi Babban Rashi: Shugaba Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Sarkin Ningi

An Yi Babban Rashi: Shugaba Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Sarkin Ningi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Ningi, marigayi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya
  • Shugaba Tinubu ya yiwa al'ummar masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi ta'aziyyar rasuwar basaraken wanda ya rasu a ranar Lahadi, 25 ga watan Agustan 2024
  • Ya bayyana marigayin a matsayin haziƙin shugaba wanda ya yi amfani da mulkin da Allah ya ba shi wajen hidimtawa al'ummarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Shugaba Tinubu ya jajantawa al’ummar masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar marigayin wanda ya rasu a wani asibiti da ke jihar Kano bayan ya daɗe yana fama da yunwa a ranar Lahadi, 25 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai sake shillawa ƙasar waje awanni kaɗan bayan ya dawo Najeriya

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Ningi
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Ningi Hoto: Ibrahim Malam Goje
Asali: Facebook

Tinubu ya yi ta'aziyyar Sarkin Ningi

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin haziƙin shugaba wanda ya yi amfani da sarautarsa ​​wajen yiwa al’ummarsa hidima.

Shugaban ƙasan ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma jajantawa iyalansa da dukkanin masu alhinin rasuwarsa.

"Shugaban ƙasa ya bayyana marigayin a matsayin haziƙin shugaba wanda ya yi amfani da sarautarsa wajen yiwa al'ummarsa hidima."
"Shugaban ƙasa ya yi addu'ar Allah ya jiƙan marigayi Sarkin Ningi tare da jajantawa iyalansa da dukkanin waɗanda ke alhinin rasuwarsa."

- Ajuri Ngelale

Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sanata

A wani labarin kuma, kun ji cewa masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sarautar gargajiya na ‘Majidadin Bauchi’ daga kan Sanata Shehu Buba Umar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya tuna da mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Zamfara

Masarautar ta ɗauki wannan matakin ne bisa zargin sanatan da rashin mutuntawa da cin mutuncin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

Sanata Shehu Umar na wakiltar mazabar Bauchi ta kudu ne a majalisar dattawa ta 10 a ƙarƙashin jam’iyyar adawa a jihar watau APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng