Kungiyar HURIWA Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Murabus, Ta Fadi Dalili
- Ƙungiyar marubuta masu kare haƙƙin ɗan Adam (HURIWA) ta nuna takaicinta kan yadda masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka
- Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya murƙushe miyagun waɗanda suka addabi mutane a ƙasar nan
- HURIWA ta kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi murabus daga kan muƙaminsa idan har ba zai iya kawo ƙarshensu ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar marubuta masu kare haƙƙin ɗan Adam (HURIWA) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya murƙushe masu garkuwa da mutane.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasan da ya yi murabus daga muƙaminsa idan har ba zai iya kawo ƙarshen miyagun ba.
HURIWA ta koka kan rashin tsaro
Daily Trust ta ce a cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar, Emmanuel Onwubiko, ya fitar a ranar Asabar, HURIWA ta nuna rashin jin daɗi kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita ta hanyar yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar HURIWA, yanayin rashin tsaro da ake fama da shi musamman ƙaruwar kashe-kashe da sace mutane na nuna cewa Najeriya ta gaza a ƙarƙashin jagorancin Tinubu.
An buƙaci Tinubu ya yi murabus
Ƙungiyar ta ce gazawar gwamnati mai ci na magance matsalar rashin tsaro shaida ce ta gazawarta wajen magance ƙalubalen tsaro yadda ya kamata.
"Mun zo lokacin da nan ba da jimawa ba masu garkuwa da mutane za su riƙa shiga gida-gida ko su fara neman mutane su biya kuɗin kariya."
"Hakan zai faru ne saboda sun tabbatar da cewa za su iya sace duk wanda suke so a kowane lokaci a duk inda yake a Najeriya."
"Idan gwamnati ba za ta iya samar da tsaro ga al'ummar ta ba, ta rasa halascinta. Saboda haka ya kamata Shugaba Tinubu ya magance matsalar rashin tsaro ko ya gaggauta yin murabus domin gwamnatinsa ta gaza wajen kare ƴan Najeriya."
- Emmanuel Onwubiko
Tinubu ya ba ƴan Najeriya haƙuri
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziƙin da ƙasar na ke fuskanta, gwamnatinsa na sane da buƙatun ƴan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori sosai wajen magance wasu ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta.
Asali: Legit.ng