Kisan Sarkin Gobir: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Zanga Zanga, Sun Fadi Dalili
- Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta cafke wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna adawa da kisan da aka yiwa Sarkin Gobir
- Mataikamin kakakin rundunar, Isah Mohammed a cikin wata sanarwa ya ce an cafke mutanen ne saboda ƙona dukiyoyi da kadarori a yayin zanga-zangar
- Ya bayyana cewa ƴan sanda ba za su zura idanu su bari ɓata gari su fake da zanga-zangar ba domin tayar da rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta kama wasu mutane saboda zanga-zangar da aka gudanar a garin Sabon Birni.
An gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, saboda kisan da ƴan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir.
Mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Iah Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Sokoto, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka cafke masu zanga-zanga?
Ya ce wasu bata-gari a garin sun yi ƙone-ƙone ciki har da ƙona gidaje 25 da gwamnatin jihar ta gina domin zama masauki ga jami’an da aka tura domin yin aiki a yankin, rahoton Daily Post ya tabbatar.
A cewar sanarwar, rundunar za ta yi bincike sosai domin bankaɗo ƙungiyoyin da suka yi zanga-zangar a garin.
"Ƴan sanda ba za su zura idanu su bari ɓata gari su tayar da hargitsi ba da sunan zanga-zanga. Duk wanda aka samu yana da hannu a zanga-zangar zai fuskanci fushin hukuma."
- ASP Isah Mohammed
Karanta wasu labaran kan kisan Sarkin Gobir
- Zanga zanga ta barke kan kisan Sarkin Gobir, bayanai sun fito
- Sanatocin Arewa sun fusata, sun yi tofin Allah tsine kan kisan Sarkin Gobir
- Kisan sarkin Gobir: Sheikh Pantami ya yi bakin ciki, ya yi bakar addu'a kan miyagu
Matawalle ya magantu kan kisan Sarkin Gobir
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan hakimin Gatawa dake ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sakkwato wanda aka fi sani da Sarkin Gobir.
Matawalle ya bayyana kisan sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa a matsayin ɗanyen aiki na rashin imani, inda ya ce duk mai hannu a kisan zai ɗanɗana kuɗarsa.
Asali: Legit.ng