“Malama Wari Kike”: Bidiyon Yadda Direban Taxi Ya Kori Fasinjarsa, Ya Ce Ta Cika Tsami

“Malama Wari Kike”: Bidiyon Yadda Direban Taxi Ya Kori Fasinjarsa, Ya Ce Ta Cika Tsami

  • An taba dirama a tsakanin direban kabu-kabu na Bolt da wata matar da ta shiga motarsa don ya kai ta wani wurin
  • Direban ya yi korafi da cewa, matar ta cika tsami, don haka ya umarce ta cikin fushi ta fice masa daga mota nan take
  • A bidiyon da aka yada, an ga matar cikin fushi ta fita daga motar tare da yi masa barazanar sai ta yi maganinsa

Wani matukin motar kabu-kanu ta Bold mai suna @virginbishop ya yada wani bidiyon haduwarsa da wata fasinja mai warin kashi.

A bidiyon, an ga direban na bayyana fushinsa tare da umartar matar ta tattara kwamutshenta ta fice masa daga mota tare da cewa tana tsami.

Mai Bolt ya kori fasinjarsa saboda tana warin jiki
Yadda direban Bolt ya kori dirabarsa a mota | Hoto: @virginbishop
Asali: TikTok

Ya ce mata:

“Malama kada ki fusata, kina dauke da wani abu da ke wari ne? Warin ya yi yawa.”

Kara karanta wannan

An shiga jimami, tirela ta markaɗe tsohuwa da jikarta har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Jikinki na wari malama”, mai Bolt ya zargi fasinja

Daga nan ne matar ta yi martani da cewa, bata dauke da komai amma mai Bolt ya ki amincewa. Ya zarge ta da watakila tana da warin kashi.

Sai yace mata:

“To watakila jikinki ne ke wari. Na gaji da jurewa. Warin ya yi yawa kuma ba zan iya jurewa ba yanzu kam.”

“Ba za ka iya sayen turare na ba”, martanin fasinja

Wannan batu na direban Bolt ya fusata hajiya fasinja, inda ta yi alfaharin cewa, ba zai iya sayen nau’in turaren da take amfani dashi amma a haka yake ce mata mai warin kashi.

Hakazalika, ta yi kokarin hana shi daukarta bidiyo, amma a haka ya dauke tare da bayyana cewa, wannan shaidarsa idan ta kai kararsa a ofishin Bolt.

Daga nan ya ce ta fice masa daga mota, haka kuma aka yi, inda ta fita tana ruga masa ashariya. Direban bai karbi kudinta ba. Wannan lamari ya faru ne a birnin Fatakwal ta jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Bayan kashe sarkin Gobir, 'yan bindiga sun saki bidiyon matan Neja 26 da suka sace

Jama'a a kafar sada zumunta basu ji dadin martaninsa ba, sun ce ya fada mata mummunar magana kuma bai dace ba.

Wasu kuwa sun bayyana yadda su ma suke fama da yanayin da ya shiga a ayyukansu na tuki ko akasin haka.

Yadda aka kori mutum a jirgi saboda warin kashi

A wani labarin, wani mutumi mai suna Yossi Adler, matarsa Jennie da diyarsu sun shiga wani jirgin sama amma sai aka fatattake su bayan sauran fasinjoji sun yi korafin cewa suna mugun wari.

Mutumin ya koka cewa kamfanin jirgin bai yi masa da iyalinsa adalci ba kuma basu samu yin tafiyar yadda suka tsara ba.

Ya bayyana cewa an nuna musu wariya saboda addininsu don su Yahudawa ne, rahoton Daily Mirror.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.