Dan Majalisa Ya Maida Martani Bayan Ɗan Sarkin Gobir Ya Faɗi Wanda Ya Sa a Kashe Babansu

Dan Majalisa Ya Maida Martani Bayan Ɗan Sarkin Gobir Ya Faɗi Wanda Ya Sa a Kashe Babansu

  • Ɗan majalisar dokokin Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza ya musanta zargin hannu a garkuwa da marigayi Sarkin Gobir
  • A wani faifan bidiyo, ɗan marigayi sarkin ya bayyana abin da ƴan bindiga suka faɗa masu kafin su kashe babansu, Isa Muhammad Bawa
  • Aminu Boza ya mayar da martanin cewa zargin wata makarƙashiya ce kuma a yanzu ya ɗaura ɗamarar yaƙi da ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Boza ya musanta zargin hannu a garkuwa da kisan Sarkin Gobir.

Idan baku manta ba ƴan bindiga sun sace sarkin Gobir hakimin Gatawa da ke aramar hukumar Sabon Birni, Isa Muhammad Bawa tare da ɗansa a watan jiya.

Kara karanta wannan

Boko Haram zuwa 'yan bindiga: Manyan sarakuna 3 da 'yan ta'adda suka hallaka a Najeriya

Marigayi Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa.
Dan majalisar jihar Sakkwato ya musanta hannu a kisan Sarkin Gobir Hoto: Abbakar AI
Asali: Facebook

Tribune Online ta tattaro cewa masu garkuwan sun kashe basaraken duk da an kai masu kuɗin fansar da suka buƙata, wannan lamari ya girgiza ƴan Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan sarkin Gobir ya fara tone-tone

Bayan kisan sarkin, ɗaya daga cikin ƴaƴansa wanda aka sace su tare ya yi zargin cewa Hon. Aminu Boza na da hannu a kitsa sace marigayi Sarkin Gobi da kashe shi.

A cewarsa, ‘yan fashin da suka sace mahaifinsa suka kashe shi sun faɗa masa ɗan majalisar ya ba su muhimman bayanai kana ya biya su N5m don su wulaƙanta sarkin.

A cikin wani faifan bidiyo, an ga dan marigayi Bawa yana kwance a gadon asibiti ana masa magani, yana ba da cikakken bayani kan ikirari da barayin suka yi.

"A gabana ƴan bindigar suka ce Aminu Boza ne ya ba su bindigun da suka yi garkuwa da mu, an ba su makaman ne a lokacin kamfe.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir ya harzuƙa Gwamnatin Tinubu, minista ya ba sojoji umarnin gaggawa

"Sun shaidawa babanmu (kafin su kashe shi) cewa ba su ma san shi ba, amma N5m aka ba su domin su yi garkuwa da shi."

Aminu Boza ya mayar da martani

Da yake martani a wani saƙon murya, Hon Aminu Boza ya musanta hannu a kowane irin aikin laifi ko alaƙa da ƴan bindiga.

“Ina tabbatar da cewa wadannan zarge-zargen ba za su taɓa sa na karaya ba wajen yaki da ‘yan fashin daji, kamar yadda na sha faɗa dole mu haɗa kai mu yaƙe su."
"Har gobe ina kan bakata ka da gwamnati ta yi sulhu da su, waɗannan ƴan bindigar ba abin yarda ba ne. Na san cewa yaƙi da su da abu ne mai sauƙi ba.
"Amma ko da na rasa rayuwata a kokarin kawar da ƴan bindiga, zan gamsu cewa na mutu ne a kokarin kare mutane na."

Matawalle ya ɗauki mataki kan kisan Sarkin Gobir

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga suka karɓi kuɗin fansa sama da N50m duk da kashe Sarkin Gobir

Rahoto ya zo cewa gwamnatin tarayya ta umarci rundunar sojojin Najeriya ta farauto waɗanda suka kashe sarkin Gobir a Sakkwato, Muhammad Isa Bawa.

Ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle ya yi tir da kisan, yana mai cewa dukkan masu hannu a wannan rashin imanin za su ɗanɗana kuɗarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262