An Shiga Jimami, Tirela Ta Markaɗe Tsohuwa da Jikarta har Lahira

An Shiga Jimami, Tirela Ta Markaɗe Tsohuwa da Jikarta har Lahira

  • An samu mummunan hadarin babbar mota a jihar Ogun inda wata tsohuwa da jikarta suka rigamu gidan gaskiya
  • Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa hadarin ya faru ne sakamakon kaucewa doka da matukin babbar motar yayi
  • Tuni matasan yankin suka garzaya da sauran wadanda suka samu munanan raunuka zuwa asibiti domin karɓar magani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - An samu haɗuran mota a jere a jihar Ogun inda aka samu mutuwa da raunata mutane da dama.

An ruwaito cewa hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata tsohuwa tare da jikarta inda babbar mota ta markaɗe su har lahira.

Hadarin mota
Hadarin tirela ya rutsa da tsohuwa a Ogun. Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami'i mai kula da zirga zirgar abubuwan hawa ya ce matukin babbar motar ya saɓa doka.

Kara karanta wannan

Daga zuwa hawan dutse, dalibi ya fadawa ajalinsa a tafkin kiwon kifi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tirela ta markade tsohuwa

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa matukin babbar motar ya yi kokarin shan kan Keke NAPEP da wasu mutane ke ciki sai rana ta ɓaci.

Matukin na kokarin wuce mai Keke NAPEP din ne sai ya doke ta har kasa daga nan sai ya taka ta inda ya markade mutanen ciki har da tsohuwa da jikarta.

Marasa lafiya na kwance a asibiti

Daily Trust ta wallafa cewa bayan hadarin, wasu daga cikin matasan yankin sun yi gaggawar mika waɗanda suka ji raunuka asibiti domin ceto rayukansu.

Bayan haka, rundunar yan sandan jihar Ogun ta mika gawar tsohuwar da jikarta ga iyalansu domin a musu janaza.

An kama direban da ya kashe tsohuwa

Bayan latse tsohuwa da jikarta, an ruwaito cewa matukin babbar motar ya gudu kafin a bi shi a kamo shi daga baya.

Kara karanta wannan

Alkali ta yi afuwa ga fursunoni 44, ta gargadi ɓarawon tukunyar mahaifiyarsa

Rundunar yan sanda ta mika jaje ga iyalan wadanda suka rasu tare da yin gargadi ga masu abubuwan hawa kan nisantar tukin ganganci.

An yi hadarin tirela a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kwaryar jihar.

Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta yi gamsasshen bayani kan yadda haɗarin ya faru da irin hasarar rayuka da dukiya da aka tafka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng