Kano: Binciken PCACC Ya Fadada yayin da Aka Tsare Ciyamomi 3 da Wasu Mutum 19
- Hukumar da ke yaƙi da cin hanci a Kano na ci gaba da bincike kan badakalar kwangila da ake zargin an yi a jihar
- PCACC ta tsare wasu shugabannin ƙananan hukumomi uku bisa zarginsu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen
- Majiyoyi sun bayyana shugabannin sun amsa cewa sun karkatar da kuɗin zuwa asusunsu yayin da aka fara ƙwato wasu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta tsare wasu shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi uku bisa zargin badaƙalar kwangilar ruwa ta N660m.
Hukumar ta kuma ba da belin Musa Garba Kwankwaso, da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis bayan ya bayyana a gabanta.
Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyi sun ce an umarce shi da ya koma ofishin hukumar a ranar Litinin mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu Ciyamomin Kano sun amsa laifinsu
Majiyoyin sun ƙara da cewa shugabannin ƙananan hukumomin uku da ake bincika sun amsa cewa sun karkatar da kuɗaɗe zuwa asusunsu.
Shugabannin sun haɗa da na ƙaramar hukumar Kiru, Abdulaziz Sulaiman, Basiru Abubakar na ƙaramar hukumar Bebeji da Gambo Isa na ƙaramar hukumar Garko.
An tsare ƙarin wasu da ake zargi
Har ila yau, mutane 19 a halin yanzu suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi. Mutanen sun haɗa da masu ajiyar kuɗi da sauran jami'an gwamnati na ƙananan hukumomin.
Ana zargin su da hannu wajen tura kuɗaɗe zuwa asusunsu sannan a wasu lokutan ciro tsabar kuɗaɗen.
An ƙwato wasu miliyoyi daga hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin ƙwato sauran.
Hukumar PCACC ta ba da beli?
Hukumar PCACC ta bayar da belin shugabannin ƙananan hukumomin amma ba su cika sharuɗɗan belin ba.
Sai dai, rahoton ya ce za a bayar da belin su a hukumance da zarar sun cika sharuɗɗan.
Ɗan uwan Kwankwaso zai je kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Musa Garba Kwankwaso ɗan uwa ga madugun tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan binciken da hukumomi ke yi masa.
Musa Garba Kwankwaso ya ce zai garzaya kotu domin ƙalubalantar matakin da hukumomin na yaƙi da cin hanci da rashawa har guda uku suka ɗauka na bincikarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng