Zanga Zanga Ta Yi Tasiri, Gwamnatin Tinubu Ta Tashi Tsaye kan Koken Ƴan Najeriya

Zanga Zanga Ta Yi Tasiri, Gwamnatin Tinubu Ta Tashi Tsaye kan Koken Ƴan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zanga-zangar da aka yi ta ƙara tunatar da ita bukatar yawan sauraron koken jama'a
  • Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa ya ce a yanzu gwamnati na zama ta saurari koken ƴan Najeriya fiye da a baya
  • Atiku Bagudu ya ce Bola Tinubu ya gano kura-kuran gwamnatocin da suka gabata, amma ba ya son ɗorawa kowa laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Atiku Abubakar Bagudu, ya ce zanga-zangar yunwa da aka yi ta tilasta masu kara buɗe kunne don jin koken ƴan Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa zanga-zangar ta zaburar da gwamnatin tarayya tare da tuna mata ta riƙa sauraren koke da halin da ƴan ƙasa ke ciki.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya tsoma baki, ya haskawa gwamna hanyar kawo ƙarshen ƴan bindiga

Ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu.
Atiku Bagudu ya ce zanga-zanga ta ƙara ankarar da gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Atiku Bagudu
Asali: Twitter

Bagudu ya ce duk da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gano kura-kuran da gwamnatocin baya suka tafka, ba ya son a zargin kowa kan halin matsin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Bagudu ya yi wannan furucin ne a wurin wani taron tattain arziki da ya gudana a Abuja, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Gwamnatin Tinubu ta ƙara azama

Ministan ya ƙara baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa gwamnati ta tashi tsaye, kuma tana kan ƙoƙarin dawo da Najeriya kan turba mai kyau, Ripples Nigeria ta rahoto.

A kalamansa Bagudu ya ce:

"Mun fahimci cewa wannan zanga-zanga da aka yi ta tashe mu daga barci, mu na sauraron koken jama'a fiye da a baya. Mun gane duk abin da muka tasa ya kamata mu zage dantse.
"Shugaban ƙasa ya kalli duka abubuwan da suka faru a baya kuma ba ya son ɗorawa kwa laifi. A zahirin gaskiya duk da ƙoƙarin gwamnatocin baya, ba mu kai inda ya kamata a ce mun kai ba."

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

Atiku Bagudu ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta tsaya surutun wane ke da laifi ko wane ba, za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Rikicin Rivers ya dawo ɗanye

Kun ji cewa alamu sun nuna babu ranar sasanta rikicin siyasar jihar Ribas yayin da ƴan NWC PDP suka fara haɗa kai da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rahotanni sun nuna rikicin ya raba kawunan shugabannin PDP na ƙasa, tsagi ɗaya na tare da Wike yayin da sauran ke goyon bayan Simi Fubara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262