Mutumin Jonathan Ya Tono Makircin da Ake Shiryawa Tinubu a Arewa kan Sayen Jirgin Sama

Mutumin Jonathan Ya Tono Makircin da Ake Shiryawa Tinubu a Arewa kan Sayen Jirgin Sama

  • Tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan ya sha rubdugu wajen matasa yayin da yake kare gwamanti kan sayen jirgin sama
  • Reno Omokri ya caccaki wasu yan jarida kan zargin suna matsin lamba ga shugabannin Najeriya da suka fito daga Kudu
  • Ya kuma yi nuni da cewa shugaban Iran ya mutu a hadarin jirgi wanda hakan ke ishara da bukatar sayen jirgi domin kiyaye lafyar Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon jami'in shugaba Goodluck Jonathan ya sha rubdugu wajen matasa a shafin X bayan ya yi kokarin kare sayen jirgin Bola Tinubu.

Reno Omokri ya nuna cewa an soki Bola Tinubu kan sayen jirgin ne saboda shi ba dan Arewa ba ne.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nemi hakkin 'yan kasa, ya bukaci bayanan sabon jirgin Tinubu

Reno Omokri
An caccaki Reno Omokri kan ba Tinubu kariya. Hoto: Reno Omokri|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Reno Omokri ya yi magana ne bayan an nuna yadda Amurka ta ke amfani da jirgin shugaban kasa daya a shekaru 34 babu canji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baaba ya ce dole talakawa su yi korafi

Bayan Reno Omokri ya wallafa rubutun ba Tinubu kariya a X, wani mai amfani da kafar X, @Baabajnr ya ce rashin biyan bukatun talakawa ne zai sa su korafi.

@Baabajnr ya bayyana cewa da a ce Bola Tinubu ya samar da abubuwan more rayuwa ga talakawa da ba za su yi wani martani ba kan sayen jirgin.

Julius: 'Ba a yiwa Tinubu fatan haɗari'

Julius Ogedengbe ya ce korafin da talakawa ke yi ba yana nufin fatan mutuwa ga Bola Tinubu ba ne sai dai ana nuna masa halin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun adawa sun hada kai, sun ragargaji Tinubu kan sayen sabon jirgi

Ya ce yan jarida da suka bankado labarin sayen jirgin sun yi gaskiya, wannan ba lokacin da ya kamata a saye jirgin shugaban kasa ba ne.

Reno na neman muƙamin gwamnati?

Wani mai amfani da kafar X, @Mrmarcelpen ya rubuta cewa ko Reno Omokri yana neman wani abu a wajen gwamnati ne, idan yana nema Allah ya ba shi.

@Mrmarcelpen ya kara da cewa yadda Reno Omokri yake kokarin kare gwamnatin Bola Tinubu ya nuna akwai alamar wani zance a bayan fage.

Tallafin mai: Oby ta ba Tinubu shawara

A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar ministar ilimi, Dakta Oby Ezekwesili ta shiga sahun waɗanda suka yi magana a kan cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi.

Oby Ezekwesili ta ce cire tallafi kawai ba zai kawo sauyi a tattalin Najeriya ba har sai shugaban kasa ya kara daukan wasu matakai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng