Matawalle Ya Tuna da Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Ritsa da Su a Zamfara

Matawalle Ya Tuna da Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Ritsa da Su a Zamfara

  • Bello Matawalle ya ba da tallafi ga mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a garin Gummi na jihar Zamfara
  • Ƙaramin ministan tsaron na Shugaba Bola Tinubu ya ba da tsabar kuɗi N20m domin rabawa mutanen da lamarin ya shafa
  • Matawalle ya buƙace su da su rungumi ƙaddara tare da fatan samun abin da yafi wanda suka rasa daga wajen Allah (SWT)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayar da tallafin kuɗi N20m ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa da ya shafa a jihar Zamfara.

Bello Matawalle ya bayar da tallafin ne a ranar Talata sakamakon ambaliyar da ta auku a garin Gummi na jihar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya tsoma baki, ya haskawa gwamna hanyar kawo ƙarshen ƴan bindiga

Matawalle ya ba da tallafi a Zamfara
Matawalle ya ba da tallafin N20m saboda ambaliya a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Ministan ya kuma jajanta musu saboda yadda suka yi asarar gidaje, dabbobi, kayan abinci, da gonakinsu, sakamakon ruwan saman da aka samu a yankin, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya ba da tallafin ambaliya

An isar da saƙon da gudunmawar ministan ne ta hannun wata tawaga mai mutum 21 ƙarkashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Tukur Danfulani, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Matawalle ya buƙaci mutanen da ambaliyar ta shafa da su ɗauki halin da suke ciki a matsayin ƙaddara daga Allah kuma su yi fatan ya musanya musu da abin da yafi wanda suka rasa.

Tukur Danfulani, wanda ya yi jawabi a yayin ziyarar, ya yi addu’ar Allah ya kiyaye aukuwar irin wannan bala’in, sannan ya miƙawa Sarkin Gummi, Mai Shari’a Lawal Gummi (mai ritaya) tsabar kuɗi N20m domin rabawa waɗanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

An yi kira ga masu hannu da shuni

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da su taimakawa waɗanda ambaliyar ta Gummi ta shafa da sauran wuraren da aka samu a jihar da kayayyakin agaji da tallafi.

Da yake karbar tallafin, Sarkin ya nuna godiyarsa ga ministan bisa tallafin gaggawar da ya yiwa jama’arsa.

Matawalle ya yi fallasa ƴan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya koka kan masu kokarin kayar da Bola Tinubu a 2027.

Bello Matawalle ya ce yan siyasa masu nuna bani-na-iya ne masu son juyawa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya a yankin Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng