Gwamnan Plateau Ya Dakatar da Manyan Jami'an Gwamnati Mutum 4

Gwamnan Plateau Ya Dakatar da Manyan Jami'an Gwamnati Mutum 4

  • iMai grma Gwamnan jihar Plateau ya ɗauki matakin dakatar da wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa
  • Caleb Mutfwang ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu manyan jami'an gwamnati mutum biyu daga kan muƙamansu
  • Sakataren yaɗa labaran gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ƙara da cewa dakatarwar ta fara aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Barista Caleb Mutfwang, ya amince da dakatar da wasu manyan jami'an gwamnatinsa guda huɗu daga kan muƙamansu.

Gwamna Mutfwang ya dakatar da kwamishinoni biyu, babban mai ba shi shawara na musamman sai kuma wani jami'in gwamnati.

Gwamnan Plateau ya dakatar da kwamishinoni
Gwamnan Plateau ya dakatar da kwamishinoni biyu Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gwamnan, Mista Gyang Bere, ya fitar a ranar Talata ta tabbatar da hakan, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa daga PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Plateau ya dakatar da kwamishinoni

Sanarwar ta ce jami’an da abin ya shafa sun haɗa da kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Honorabul Chrysanthus Dawm, da kwamishinan yawon buɗe ido da al'adu Honorabul Jamila Tukur.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Honorabul Dio Lamul, mai ba da shawara na musamman kan raya karkara, da Honorabul Moses Sule, jami’in hulɗa da jama’a na mazaɓar Mikang.

Ko da yake ba a bayar da dalilin dakatar da su daga muƙamansu ba, amma sanarwar ta ce dakatarwar da aka yiwa manyan jami’an na gwamnati guda huɗu ta fara aiki ne nan take.

Karanta wasu labaran kan jihar Plateau

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya

Gwamnan Plateau ya kashe N3.9bn kan motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Plateau ta ƙaryata zargin da ake yi na cewa ta ware N3.9bn domin siyan motocin alfarma.

Kuɗin da ke ke wakiltar kaso 47% na kuɗin da za a kashe a jihar an ce an fitar da su ne a watanni uku na farkon shekarar 2024 domin siyo motocin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng