Abubuwa 3 da Suka Faru a Najeriya bayan Buhari da Jonathan Sun Gana da Tinubu

Abubuwa 3 da Suka Faru a Najeriya bayan Buhari da Jonathan Sun Gana da Tinubu

  • A makon da ya wuce ne tsofaffin shugabannin Najeriya suka taru a fadar shugaban kasa domin taron majalisar magabatan kasa
  • Biyo bayan taron, akwai abubuwa da dama da suka biyo baya a Najeriya wanda kuma sun ja hankulan al'umma a fadin ƙasar nan
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu daga cikin abubuwan da suka faru a kasa da mako daya bayan taron majalisar magabata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tun bayan ganawar da Buhari da Jonathan suka yi da Tinubu a taron magabata abubuwa da dama sun faru a Najeriya.

Zancen maido tallafin man fetur da ya fito a yau Litinin na cikin abubuwan da suka ja hankulan yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi bayan kotun turai ta saka Najeriya a gaba kan jirage 3

Taron magabata
Abubuwan da suka faru bayan taron magabatan kasa. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro abubuwa uku da suka faru a Najeriya kuma suka ja hankula tun bayan taron majalisar magabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kwace jiragen shugaban kasa a Faris

A makon da ya wuce labari ya bazu a kafafen sadarwa kan cewa wani kamfani a kasar Sin ya samu izinin kwace jiragen shugaban kasar Najeriya.

Lamarin ya ja hankulan al'umma cikin har da manyan yan siyasa inda suka rika sukar gwamnatin Najeriya da ta jihar Ogun kan rashin tsari.

2. Batun sayen sabon jirgin shugaban kasa

Wasu masu sharhi na ganin cewa gwamnatin tarayya ta fito da maganar kwace jiragen shugaban kasa ne domin samun hanyar sayen sabon jirgi ga Bola Tinubu.

Ana haka sai aka ji labarin cewa gwamnatin tarayya ta saye sabon jirgi wanda Legit ta ruwaito cewa an karya dokar majalisa wajen sayensa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kuma gamuwa da cikas bayan kwace jiragen fadar shugaban kasa 3 a ketare

Wanna lamari ya ja hankulan yan Najeriya musamman lura da yadda ake ciki a Najeriya ace an saye sabon jirgi ga shugaban kasa.

3. Maganar maido tallafin man fetur

Legit ta ruwaito sabon zance kan cewa Bola Tinubu ya ba kamfanin NNPCL izinin maido tallafin man fetur.

Sai dai lamarin ya ja hankulan al'umma kasancewar Bola Tinubu ya sha nanata cewa ba zai dawo da tallafin mai ba.

A yanzu haka dai yan kasa sun kasa kunnuwa su ji ko gwamnatin tarayya za ta yi karin haske kan lamarin.

APC za ta yi taron matasan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da matasan Najeriya har 3,000 domin tattaunawa kan kawo cigaba a fadin ƙasar nan.

Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ne ya fitar da sanarwa kan yadda taron zai gudana a fadar shugaban kasar Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng