Matatar Ɗangote: Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauki Matakin Sauke Farashin Fetur a Najeriya

Matatar Ɗangote: Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauki Matakin Sauke Farashin Fetur a Najeriya

  • Ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 gwamnatin tarayya za ta fara sayarwa matatar Aliko Ɗangote da ɗanyen mai a Naira
  • Ministan kuɗi ya bayyana haka a taron kwamitin da aka kafa domin aiwatar da umarnin shugaban ƙasa a yau Litinin
  • Shugaban hukumar tattara haraji ya ce a watan gobe ake sa ran fetur da aka tace a matatar Ɗangote zai shiga kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta ce ranar 1 ga watan Oktoba, za ta fara sayarwa matatar Ɗangote da ɗanyen mai a Naira.

Gwamnatin ta ce an cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin da aka kafa don aiwatar da sayar da ɗanyen mai a Naira karkashin ministan kudi, Wale Edun.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kotun Koli ta fara zaman karshe kan shari'ar zaben gwamnan Kogi da Bayelsa

Wale Edun.
Matatar Ɗangote: Gwamnati tarayya za ta fara sayarwa Ɗangote da ɗanyen mai a watan Oktoba Hoto: Wale Edun
Asali: UGC

Ma'aikatar kuɗi ta tarayya ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 19 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 15 ga watan Agusta ne aka kaddamar da wani karamin kwamiti na fasaha domin aiwatar da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na sayar da danyen mai ga matatun cikin gida a Naira.

Ana hasashen wannan matakin zai sauke farashin man fetur wanda ya ƙara tsaɗa tun bayan cire tallafi a Najeriya.

Yaushe za a fara saidawa Ɗangote mai?

A taron kwamitin na yau Litinin, Wale Edun ya tabbatar da cewa za a fara cinikayyar ɗanyen mai da Naira daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

"Daga cikin muhimman batutuwan da kwamitin ya tattauna a taron har da batun sayarwa matatar Ɗangote ɗanyen mai a kuɗin Najeriya wanda za a fara a watan Oktoba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace kwamishina da matarsa a hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar gwamna

"Har ila yau an gabatar da bayanai game da matatar Fatakwal da kuma sabuwar matatar attajirin nan, Aliko Ɗangote, ana sa ran tace mai zai ƙaru a watan Nuwamba."

Man Ɗangote zai shiga kasuwa

A nasa jawabin a wurin taron, shugaban hukumar tara haraji FIRS, Zacch Adedeji, ya ce a watan gobe man fetur daga matatar Ɗangote zai shiga kasuwa.

Ana hasashen farashin fetur zai karye

A wani rahoton kuma ƴan kasuwa sun yi hasashen samun sauƙin farashin man fetur yayin da ake tsammanin fara samun tataccen mai daga matatar Dangote.

Mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwar man fetur ta kasa (IPMAN), Hammed Fashola ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262