Matsala Ta Tunkaro Tinubu Yayin da Shirye Shiryen Sabuwar Zanga Zanga Suka Yi Nisa

Matsala Ta Tunkaro Tinubu Yayin da Shirye Shiryen Sabuwar Zanga Zanga Suka Yi Nisa

  • Masu shirya gudanar da zanga-zanga ba su haƙura ba kan buƙatun da suke neman gwamnatin tarayya ta biya musu
  • Masu shirya zsnga-zangar wacce aka gudanar a tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta, sun ce za a sake fitowa a Oktoba
  • Hakazalika ana ci gaba da ƙoƙari wajen ganin an sako mutanen da aka kama lokacin da ake gudanar da zanga-zangar baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Masu shirya zanga-zangar #EndBadGovernance a Najeriya da aka kammala sun fara shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a ƙasar nan.

Masu shirya zanga-zangar na shirin sake fitowa kan tituna ne a cikin watan Oktoban 2024 da ke tafe.

Za a yi sabuwar zanga zanga a watan Oktoba
An fara shirin gudanar da sabuwar zanga zanga a Najeriya Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Wani darakta na ƙungiyar 'Take It Back Movement', Damilare Adenola, ya tabbatarwa jaridar The Punch hakan a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Farfesa ya hango abin da zai tayar da hankalin Tinubu, ya yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi sabuwar zanga-zanga a Najeriya

Damilare Adenola ya ce ba za su sauya buƙatun da suke gwamnati ta biya musu ba, idan dai har ba buƙatar hakan ba ce ta taso ba.

"Eh gaskiya ne. Mun sanya mata sunan ‘Fearless in October Protest’. Buƙatunmu za su kasance iri ɗaya ne. Sai dai ƙila mu ƙara wasu yayin da ƙasar nan ke ci gaba ta taɓarɓarewa a kullum."

- Damilare Adenola

Da aka tambaye shi ko za su bi umarnin kotu a wasu jihohi na cewa su yi zanga-zanga a wasu keɓaɓɓun wurare, Damilare ya bayyana cewa ba za su mutunta wannan umarnin ba.

Ana ƙoƙarin ceto waɗanda aka kama

Haka kuma, wani ɗan gwagwarmaya kuma lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju ya bayyana cewa a halin yanzu ana ƙoƙarin ganin an sako masu zanga-zangar da aka kama.

Kara karanta wannan

Ba a gama farfadowa ba, an shirya gudanar da sabuwar zanga zanga a Najeriya

"Muna ci gaba da dukkanin ƙoƙarin da ya kamata domin ganin an sako mutanen da aka kama."

- Deji Adeyanju

Tinubu ya gargaɗi masu zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zanga-zangar #Endbadgovernance da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da su gaggauta dakatar da zanga-zangar su fito domin a tattauna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng